Hukumar EFCC ta bayyana cewa ta kai samame wani gidan rawa da holewa, inda ta kama kusan mutane 100 da ta ke argi da damfara, a Jihar Osun.
Wannan bayani da ya fito a yau Litinin, ya tabbatar da cewa kulob din wanda aka kai harin a garin Osogbo, babban birnin Jihar Osun, an ce ya yi kaurin suna inda masu damfara ke suka maida shi wajen shirya dabdalar su.
EFCC ta ce an kama mutane 94 tare da kama motoci 19, kwamfutar laptops, manyan wayoyin hannu da sauran kayayyaki daban-daban.
PREMIUM TIMES ta kasa tabbatar da takamaimen abin da ya faru yayin wannan farmaki da EFCC ta kai, wanda shi ne na farkon da ta fi kama mutane masu yawa haka a lokaci daya.
Kulob din wanda aka fi sani da suna ‘Club Secret Underground’, ya na kan babban titin Ibadan zuwa Iwo, cikin garin Osogbo.
“Kamen da aka yi cikin talatainin dare ya biyo bayan wani rahoton sirri da EFCC ta samu cewa ‘yan damfarar sun shirya wata kasaitacciyar dabdala a ranar Lahadi da dare, 13 Ga Oktoba, domin murnar wata gagarimar damfara ta makudan kudade da suka yi.”
Haka dai kakakin yada labarai na kasa na EFCC, Wilson Uwujaren ya bayyana.
Ya ce wadanda ake zargin duk ana ci gaba da binciken su. Kuma da zarar an kammala duk za a gurfanar da su a kotu.
Discussion about this post