Daya daga cikin manyan bakin da za su tattauna game da matsalolin dake hana samun ci gaba a fannin kiwon lafiyar kasar nan Dakta Dale Ogunbayo ya yi kira ga mutane da su rika yin tambayoyi game da yadda ake kashe kudaden da gwamnati ke ware wa fannin kiwon lafiya.
Ogunbayo fadi haka ne da yake hira da PREMIUM TIMES a shirin taron tattauna matsalolin dake cu wa fannin kiwon lafiya tuwo a kasar nan.
Za a gudanar da wannan taro ne daga ranar 15 zuwa 16 ga wannan wata na Oktoba a Otel Nicon Luxury dake Abuja.
An gayyaci masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya domin ganin yadda tallaka a Najeriya zai iya samun kiwon lafiya na gari a farashi mai sauki.
Ogunbyo ya kara da cewa aza a smu nasara a haka ne idan mutane na bibiyar yadda ake kashe kudaden maimakon a barsu a hannun mahukunta suna yin abin da suka ga dama da kudaden jama’a.
“A yanzu haka kudaden da gwamnati ke ware wa fannin kiwon lafiya basu isan fannin sannan duk shekara gwamnati na kara rage wadannan kudade maimakon a kara yawan su.
A karshe yayi kira ga gwamnati da ta maida hankali wajen kara ware wa fannin kiwon lafiyan kudade masu kauri domin ci gaban fannin da kuma gyara fannin.
Discussion about this post