’Yan Najeriya da aka yanke wa hukuncin kisa a kasar Malaysia, kuma su na jiran a zartas da kisan a kan su, sun fi ‘yan sauran kasashen duniya yawa. Kungiyar Jinkai ta Duniya, Amnesty International ce ta bayyana haka a yau Litinin.
Daga cikin baki ‘yan kasashen waje su 568 da ke daure kuma aka yanke musu hukuncin kisa a Malaysia, 119 duk ‘yan Najeriya ne. Haka dai rahoton na Amnesty International (AI) ya tabbatar.
Gaba daya dai a kasar akwai mutane 1,281 da aka yanke wa hukuncin kisa, kuma su na tsare a cikin kurkuku 26, kamar yadda binciken da aka gudanar tun a ranar 22 Ga Fabrairu ya nuna.
A kasar Malaysia dai akwai laifuka 33 wadanda duk wanda mutum ya aikata daga cikin su, to hukuncin kisa za a zartas a kan sa.
Akasarin wadanda aka yanke wa hukuncin kisan dai duk laifuka ne da suka danganci safarar kwayoyi.
Sauran laifukan kuma akwai amfani da mugun makami, fashi da makami, kaddamar da yaki a kan sarkin kasar ko shugaban jiha.
’Yan Najeriya ne suka fi yawan masu jiran a kaddamar da hukuncin kisa a kan su. Sannan sai Indonesia, Iran, Indiya, Philippines da Thailand.
Rahoton ya nuna cewa akwai ‘yan Najeriya da dama da ke jiran a zartas da hukuncin kira a kan su a kasashe daban-daban. Cikin watan Afrilu, an yanke wa ‘yan Najeriya 23 hukuncin kira a Saudi Arabiya.
Ba a sani ba ko Najeriya ta yi wata magana a kan wadanda ke jiran hukuncin kisa a Malaysia. Kokarin jin ta bakin jami’an Najeriya bai yi nasara ba, domin ba su dauki waya ba.
Discussion about this post