Wasu likitoci da suka kware a harkar lafiyar kwakwalwar mutum dake garin New York kasar Amurka sun bayyana cewa yawan cin gishiri a abinci na hana kaifin kwakwalwa.
Jagoran likitocin Giuseppe Faraco yace gishiri na dauke da sinadarin dake hana mutum samun kaifin kwakwalwa.
Bisa ga sakamakon binciken da likitocin suka gudanar, gishiri na sa mantuwa ta hanyar datse jini gaiwa ga kwakwalwa.
A dalilin haka likitocin suka yi kira ga mutane da su rage cin gishiri cewa yin haka na haifar da dodewar kwakwalwa da mantuwa.
Idan ba a manta ba a shekarar 2018 WHO ta yi kira ga mutane da su rage yawan cin gishiri domin guje wa kamuwa da cututtukan dake kama zuciya.
WHO ta bayyana cewa domin gujewa irin haka kamata ya yi mutane musamman matasa su ci akalla cikin karamin cokali daya ne a rana idan ya zama dole.
Idan har ta kama a ci gishiri, a rika amfani da wanda ke dauke sinadarin ‘Iodine’ domin shi wannan sinadarin na taimakawa wajen karfafa kaifin kwakwalwar yara kanana da jaririn dake cikin uwarsu.
WHO ta kuma kara da yin kira mutane da su rika rige-rigen cin kayan lambu da ganyayyaki domin bunkasa garkuwar jiki.