Babban hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai ya amince da sauyawa wasu manyan Sojojin Najeriya wuraren aiki.
A sanarwa haka da kakakin rundunar Sagir Musa ya sakawa hannu ranar Talata wannan sauye-sauye zai fara aiki ne nan take.
Wadanda aka Sauya wa aiki sun hada da:
1 – Maj.-Gen F.O Agugo – Kwamandan Barikin Soji na 6 dake Fatakol.
2 – Maj.-Gen. Jamil Sarham – Shugaban Makarantan Sojoji, NDA na Kaduna
3 – Maj.-Gen. C.O Ude – Cibiyar Nazari na rundunar Soji dake Abuja.
4 – Maj.-Gen I.M Yusuf – Kwamandan Rundunar Hadin Guiwa na sojoji dake Ndajamena
5 – Maj.-Gen. E.N Njoku – Shugaban Kirkire-kirkire da cigaba na rundunar Sojin Najeriya
6 – Brig.-Gen. E.J Amadasun – Kwamandan Barikin Soji na 35 dake Abeokuta
7 – Brig.-Gen. A.M Adetayo – Shugaban Ma’aikata na Rundunar Mayakan Soji
8 – Brig.-Gen. L.M Zakari – Kwamandan makarantan Sojoji dake Ilori
9 – Brig.-Gen. E.E. Ekpenyong – Sabon Darektan A hedikwatar Soji dake Legas
Discussion about this post