Jim kadan bayan Gwamnonin Najeriya 36 sun bayyana cewa ba za su yi auki da sharuddan yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta da Kungiyar Kwadago, NLC suka cimma wajen biyan karin albashi ba, Kungiyar Kwadago NLC ta gargadi gwamnonin Najeriya cewa ma’aikatan jihohin kasar nan za su tafi yajin aiki muddin aka tsaya ana yi musu yawo da hankali.
Jagoran tattaunawa da gwamnatin tarayya, Simon Anchaver da Sakataren NLC na Kasa, Emma Ugboaja, sun ce ba su ki ba su zauna a tattauna da kowane gwamna, domin a san iyar adadin da zai iya biya sa dai gwargwado, amma fa sai kowane gwamna ya fayyace adadin kudin da ya ke karba daga tarayya da kuma kudaden shigar da jihar sa ke samu.
Sun ce ba za su amince gwamnoni su rika yin walle-walle da batun karin albashi ba, tunda ya rigaya ya zama doka.
NLC ta yi wannan bayani ne a yau Talata, a Abuja. Ta ce bai yiwuwa gwamnoni su rika yin kumbiya-kumbiya da rufa rufa-rufar adadin kudaden da su ke karba, sannan daga baya su kawo wata magana wadda NLC ta ce ba za su lamunta a batun biyan karin albashi ba.
A jiya ne dai Gwamnonin kasar nan 36 sun tsokano wata sabuwar kwatagwangwamar biyan albashi, inda su ka bayyana cewa ba za su bi sabuwar yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta cimma tare da Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC ba.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi ne ya bayyana haka a Abuja, jim kadan bayan tashi daga wani taro da gwamnonin suka yi.
An gudanar da taron a otal din Hilton, kuma dukkan hwamnonin sun halarta.
Da ya ke jawabi a madadin sauran, Gwamna Fayemi ya ce Tarayya daban, haka kuma jihohi daban. Don haka za su koma su yi ta su mai fisshe su a kowace jiha, domin tattauna adadin da za su iya kara wa ma’aikata albashi.
Sai dai kawai ya ce gwamnoni sun amimce cewa mafi kankantar albashi ba zai yi kasa da naira 30,000, ga masu matakin albashi na 01 zuwa 06, kamar yadda sabuwar doka ta gindaya.
Amma daga mataki na 07 abin da ya kai na 17, to na za su iya yin karin kusan kashi 60 bisa 100 ba, sai dai su yi kintace su dan kara musu abin da ya saukaka kawai.
Gwamnatin Tarayya dai ta cimma cewa za ta yi karin kashi 20 bisa 100 ga masu 07 zuwa 08, sai kashi 19 ga masu 09, sai kuma kashi 16 ga masu 10 har zuwa 14.
Masu matakin albashi na 15 zuwa 17 ne aka amince za a yi wa karin kashi 14 bisa 100.
Gwamnatin tarayya ta bada umarnin a fara biyan ma’aikata sabon tsarin albashi tun daga na watan Afrilu, kuma ya kasance nan da karshen Disamba kowa ya karbi ariyas din sa ba watannin baya.
Discussion about this post