Wasu likitoci da suka kware wajen duba da masu tabuwar hankali sun koka da yadda kashe kai ke neman zama ruwan dare a Najeriya.
Bincike ya nuna cewa mutane 9.5 a cikin mutane 100,000 ke kashe kansu a Najeriya duk shekara. Sannan mutane 800,000 ne ke kashe kansu duk shekara a duniya.
Wani likita dake asibitin koyarwa na jihar Legas (LASUTH) Olayinka Atilola yace mafi yawan lokuta matsalar tabuwan hankali na daga cikin matsalolin dake sa mutum ya kashe kansa. ” A kowane sakan 30 zuwa 40 wani ko wata na kokarin kashe kansa ko kanta a fadin duniya.
Ya ce alamun tabuwar hankali sun hada da damuwa, rashin iya cin abinci, kin shiga jama’a, kin yin magana da mutane da sauran su.
Wasu hanyoyin dake sa mutum yaji Yana son ya kashe kansa sun hada da;
1. Kadaici.
2. Talauci.
3. Yawan Damuwa
4. Tsananin Soyayya.
5. Rasuwar wani makusancin da aka shaku da.
Hanyoyi 6 da za akiyaye domin gujewa fadawa cikin itin wannan marsala.
1. Samar da kula ga mutanen dake fama da tabuwar hankali.
2. A daina barin masu fama da tabuwar hankali na zama su kadai.
3. Kawar da duk wani abu da zai iya zama makami kusa da masu tabuwar hankali.
4. Jawo hankalin masu tabuwar hankali da su rika shiga mutane.
5. Karfafa guiwar su wajen cin abinci.
6. Horas da su waken koyan sana’ar hannu.
7. A guji saka Kai cikin matsanancin damuwa.