Ma’aikatar ilimi na jihar Sokoto ta rufe wasu makarantun boko masu zaman kansu har guda uku da ta kama a jihar.
Kakakin ma’aikatar Nura Maikwanci ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai a garin Sokoto ranar Lahadi.
A takardar Maikwanci ya yi bayanin cewa Ma’aikatar ta kama wadannan makarantu ne da laifin karya sharuddan kafa makarantun kudi na ma’aikatar.
Makarantu sune:
1 – Coral Foundation Spring Montessori
2 – Brighter Children’s School
3 – Godiya Nursery da Firamare
Maikwanci ya kuma ce ma’aikatar ta kuma kama wasu makarantun guda 10 da ke aiki babu lasisin gwamnati na bude makarantu masu zaman kansu ba.
Makarantun sune:
1 – Precious Nursery and Primary School
2 – Grace International School
3 – Spring-Field International School,
4 – Alkhairi International School
5 – TAC Academy Kwannawa
6 – Rhema International School
7 – Kids Ambassadors Nakasari Area
8 – Sokoto Academy
9 – De-Trend Day Care School
10 – International Academy for Excellence
Ya yi kira ga makarantun da suka samu lasisin su daga hukumar kula da ilimi ta karamar hukuma da su tabbatar sun sabunta lasisin su a ma’aikatar ilimi na jihar.
A karshe kwamishinan ilimin jihar Bello Guiwa ya bayyana cewa daga yanzu makarantun boko masu zaman kansu da suke da lasisi sannan suke bin dokokin da hukumar Kuma da makarantun me za a bari suna aiki.