A ranar Juma’a ne aka tsinci fallayen Al’kur’ani mai girma a kwatamin wata makarantar firamare maisuna makarantar Shattima dake Gusau a jihar.
A dalilin haka gwamnan jihar Bello Matawalle ya bada umurin rufe wannan makaranta tare da dakatar da malaman dake aiki a makarantar.
Matawalle ya kuma umurci hukumar kula da ilimin boko ta jihar da ta gaggauta kafa kwamitin bincike domin bankado wadanda suka aikata wannan mummunar aiki.
Sakataren gwamnatin jihar Bala Maru ya sanar da haka yana mai cewa an kafa kwamitin mutum 23 wanda a ciki akwai malaman addini, jami’an tsaro,wakilan ma’aikatu da kunguyoyi sannan Jafaru Makau ne zai jagoranci binciken da kwamitin za ta yi.
Maru ya kuma ce gwamnati za ta biya Naira miliyan biyu wa duk wanda ke da bayanai akan wanda ko wadanda suka aikata wannan mummunar aiki a jihar.
“Gwamnati ba za ta yi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wanda ko kuma wadanda aka samu da hannu a aikata wannan mummunar aiki Kuma muna kira ga mutane da su ci gaba da yin adu’o’I domin Allah ya bayyana mutanen da suka aikata haka.
Ya yi kira ga mutane da su gaggauta kai karan duk wanda suka gani a unguwanninsu da basu yards da su ba zuwa ofishin jami’an tsaro mafi kusa da su.