KADUNA: Zainab ta sha bulala 80 saboda shan Wiwi a bainar jama’a

0

Kotun dake MagajinGarin Kaduna ta yanke wa wata budurwa ‘yan Shekara 19 Mai suna Zainab Abdullahi hukuncin shan bulala 80 saboda kamata da akayi tana shan Wiwi a bainar jama’a.

Alkalin Kotun Mohammed Shehu Adamu ya bayyana cewa Zainab ta amsa laifinta wanda a dalilin haka komai ya zo wa kotun da sauki, sannan aka yanke mata hukuncin shan bulala 80 domin haka yake a doka.

Wanda ya shigar da kara ya ce an kama Zainab a titin Kaduna tana zukar Wiwi babu abinda ya dameta, hancin ta da baki na ambaliyar hayaki yadda kasan salansan mota.

Daga nan ne ‘yansanda suka garzayo da ita kotu domin a hukuntata. Sai dai kafinnan an dan tsare ta a kurkuku bayan ta kasa biyan naira 7000 na beli. Ya ce Kungiyar Musulmai na MCN ne ta fanshi Zainab daga nan sai aka kawo ta Kotu.

Alkali Shehu ya yi kira ga iyaya da malaman addinai da su maida hankali wajen kula da tarbiyyan ‘ya’yan su da kuma yin kira ga matasa dasu gujewa dabi’un da ba su da kyau.

Share.

game da Author