Majalisar Zartaswa a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ta amince da karin harajin kayayyaki, wato VAT, ko harajin jiki-magayi.
An dai amince za a kara harajin daga kashi 5 bisa 100 na duk adadin kayan da mutum ya saya cikin kasar, nan zuwa kashi 7.2 bisa 100.
Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed ce ta bayyana wannan karin a jiya Talata, lokacin da ta ke wa manema labarai, bayan fitowa daga Taron Majalisar Zartaswa, inda Shugaba Buhari ya gana da ministoci.
An yi wannan karin ne a lokacin da ake gudanar da yanke hukuncin shari’ar Atiku Abubakar da Muhammadu Buhari a kan kalubalantar sakamakon zaben 2019 da Atiku da PDP suka yi.
“Majalisa ta amince za a kara Harajin Kayayyaki (VAT), daga kashi 5 bisa 100 zuwa kashi 7.2 bisa 100.” Inji Zainab.
Zainab ta ce daya daga cikin dalilan karin kudaden harajin shi ne karin kudaden shiga na gwamnatocin jihohi.
“Yin hakan ya na da muhimmanci, saboda ita gwamnatin tarayya na daukar kashi 15 kadai na ‘VAT’ da ake tarawa. Yayin da jihohi ake raba wa kashi 85.
“A gaskiya su kuma jihohi na bukatar karin kason kudaden shiga, domin su samu su rika biyan kudaden karin mafi kankantar albashi.”
Sai dai kuma ta kara da cewa ba zai yiwu a iya aiki da sabon tsarin karin harajin ba tukunna, har sai an yi wa kundin dokar kasar nan kwaskwarima tukunna.
“Kafin a fara aiki da sabuwar dokar za a bi ana tuntuba a fadin kasar nan, sannan kuma sai an yi wa Dokar VAT kwaskwarima tukunna.
“Saboda haka ba sha-yanzu-biya-yanzu ne za a fara aiki da karin harajin ba.” Inji Zainab.
Amma kuma ta ce gwamnatin tarayya ta rigaya ta yi azarbabin saka wannan karin haraji a cikin hasashen kasafin kudaden shigar da ta ke sa ran tarawa a cikin shekarar 2020.
“Wannan kirdado ne gwamnatin tarayya ta yi, har ta yi hasashen cewa za ta tara kimanin naira tiriliyan 7.5 a cikin shekarar 2020.
“Sai kuma naira tiriliyan 2.09 da gwamnati za ta samu cikin asusun gwamnatin tarayya da kuma VAT.
Zainab ta yi karin hasken cewa gwamnatin tarayya ta yi shirin kashe naira tiriliyan 2.45 wajen biyan basusssuka a cikin shekarar 2020 har na naira tiriliyan 2.45.
“Naira tiriliyan 10.07 gwamnatin tarayya ta yi niyyar kashewa a cikin shekarar 2020 gaba daya.
Idan ba a manta ba, tun farkon hawan Zainab a matsayin minista cikin 2018 ne aka bijiro da batun karin haraji domin samar wa gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi karin kudaden shiga.
Tuni dai har jama’a sun fara nuna damuwa, musamman ganin yadda aka yi karin a ranar da Buhari ya yi nasara a kotu a kan abokin takarar sa a zaben shugaban kasa, wato Atiku Abubakar.
Karin ya zo daidai lokacin da ake kukan rufe kan iyakar kasar nan saboda hana shigo shinkafa.
A gefe daya kuma jami’an kwastan na bin direbobin da ke dauko shinkafa daga wani gari zuwa wani gari, ko da buhu uku ne su na haddasa hadurra har da asarar rayuka a kan titi.
Sannan kuma an yi karin a ranar da hukumar kwastan ta bayyana karin wa’adin rufe kan iyakokin Najeriya.