BOKO HARAM: ’Yan Najeriya 22,000 suka bace a Arewa maso Gabas – Red Cross

0

Kusan ’yan Najeriya 22,000 ne aka tabbatar da bada rahoton bacewar su a yankin Arewa maso Gabas, a tsawon shekaru goma da aka shafe ana kashe-kashen Boko Haram.

Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC) ce ta bayyana haka, tare cewa wannan adadi na cikin Najeriya shi ne mafi yawan mutanen da ake da rekod na bacewar su a duk duniya a cikin kasa daya tilo.

Haka dai ICRC ta bayyana a shafin ta a intanet a yau Alhamis.

Boko Haram ya haddasa mutuwar dubbban mutane tare da bacewar wasu dubbai, gami da asarar dimbin dukiyoyi da kuma tarwatsa milyoyin al’umma.

A cikin 2018 ne dai Kungiyar Kididdigar Ta’addanci ta Duniya, wato ‘Global Terrorism Index’ ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta uku da aka fi munin ta’addanci a duniya.

ICRC ta ce kashi 60 100 na wadannan ‘yan Najeriya 22,000 da suka bace, duk kananan yara ne a lokacin da suka salwanta din.

“Babban tashin hankalin iyaye, ba kamar a ce ‘ya’yan su su bace, ba tare da sun san inda suke ba. Wannan shi ne gaskiyar lamarin da ya faru da dubban iyayen yara, wadanda a halin yanzu an bar su cikin kuncin rayuwa da wahalar fagamniyar neman ‘ya’yan su.

“Iyaye na da ‘yancin sanin inda ‘ya’yan su suke. Sannan kuma akwai bukatar kara zage damtse wajen hana yara kanana rabuwa da iyayen su.”

Haka dai aka ruwaito Shugaban ICRC, Peter Maurer na bayyana bayan nziyarar kwanaki biyar da ya kawo Najeriya.

An ce a yayin wannan ziyara da Maurer ya kawo, ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari da wasu manyan jami’an gwamnati.

Ya kuma gana da kungiyoyin sa-kai da na kare hakkin jama’a da na jinkai. Sannan kuma ya yi magana da wasu iyalan da rikicin Boko Haram ya ritsa da a Maiduguri da Munguno. An ce da yawan su ba su san inda ‘ya’ya da ‘yan uwan su suke ba a yanzu haka.

Da yawan wadanda suka bace dai sun rabu da iyayen su ne a lokutan da Boko Haram ke kai munanan hare-hare. Wasu kuma an hakkake cewa Boko Haram ne ke kama su, su koya musu atisaye, sannan su tilasta su kasancewa zaratan yakin su, tare da daura musu bama-bamai sun a kai harin kunar-bakin-wake.

Share.

game da Author