An damke korarrun Sojojin dake badda kama da kayan sojoji suna fashi

0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta bayyana kama wani gungun masu fashi da makami na mutane bakwai, wadanda ke amfani da kakin sojoji sun a fashi da makami.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Lagos, Zubairu Mu’azu ne ya bayyana haka, tare da cewa uku daga cikin su korarrun sojojin kasa ne, yayin da biyu kuma korarrun sojojin ruwa ne.

Ya ce an samu nasarar kama su bayan sun addabi mazauna Ijegun kusa da Legas da fashi da makami.

Ya ce an dade ana neman su, domin tun a ranar 18 Ga Fabrairu ake neman su, bayan da su ka yi wa wani mutum fashin motar sa kirar Lexus RX330.

Sun kwace wa mutumin motar sa a lokacin da ya ke kan hanyar zuwa Ijegun daga Ibadan.

Sunayen korarun sojojin sun hada da; Ndidi Oluchukwu, Owolabi Adeyemo, David Olufemi, Samuel Israel, Emeka Ibeh, Samuel Anochime da kuma Ebedot Stephen.

’Yan sanda sun ce an samu wadanda aka damke din sa kayan sojoji da suke amfani da su su na yin basaja, har guda 12. An kuma same su da katin shaidar aikin soja.

Bayan nan kuma an same su da adda guda biyu, katinan cirar kudi na ATM, wukake, dan kamfai na mata da kuma wani zobe na gargajiya.

Da aka gabatar da su a gaban ‘yan jarida, Ndidi Oluchukwu, wanda korarren soja ne, ya ce dan kamfai din na matar sa ne, kuma a gidan sa ‘yan sanda suka dauko shi, a lokacin da aka kamo shi.

An dai kori Oluchukwu daga aikin soja tun cikin 2015, yayin da shafe tsawon lokacin ya yi tafiyar sa babu sanarwa kuma babu labari.

“Na dauki hutun tafiya gida saboda ba ni da lafiya a cikin 2015. Na dade ban koma aikin soja ba. Daga nan sai aka sallame ni.”

A yanzu ya ce aikin sa shi ne yi wa motocin bas-bas rakiya ana biyan sa naira 3,500 a kowace rana.

Shi kuwa korarren soja Ebedot Stephen, ya ce an kore shi daga aikin sojan ruwa ne bayan da aka same shi da tsoma hannu cikin harkallar hauma-haumar rikicin gona, wadda ya ce ya shiga ne domin ya sasanta bangarori biyu masu rikici.

Da aka tambaye shi ya aka yi ya samu kayan soja tunda shi tun tuni kokarre ne, sai ya ce wani kwamanda ya ba shi.

Daga nan kuma Kwamishinan ’Yan Sanda Mu’azu ya ci gaba da bada labarin irin nasarorin masu laifi da kuma tulin makaman da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jihar Legas ta kama a cikin dan kankanin lokaci.

Share.

game da Author