Kotu ta soke zaben ‘yan majalisa biyu a Jihar Adamawa

0

Kotun dake sauraren kararrakin zaben majalisar dokokin jihar Adamawa ta tsige yan majalisa biyu dake wakiltar shiyoyin Mubi Ta Arewa da Mubi Ta Kudu a majalisar jihar.

Duka ‘yan majalisar biyu yan jam’iyyar APC.

Na farko dai, dan majalisa Shuaibu Langa na jam’iyyar APC, kotu ta tsige shi ne saboda kama shi da tayi ya mika wa hukumar zabe takardun kammala Firamare na karya.

Kotu ta umarci hukumar zabe ta yi maza maza ta janye satifiket din da ta bashi ta mika wa Suleiman Vokna na PDP.

Langa shine ke wakiltar Mubi ta Arewa a majalisar jihar.

Langa ya soki wannan hukunci na kotu yana mai cewa bita da kulli ne ake masa.

” Yaya za a ce wai kamarni a wannan zamani wai ban kammala makarantar Firamare ba. Wannan babu gaskiya a ciki. A dalilin haka zan garzaya kotun kolu domin abi mini hakki na.

Na biyu kuma, Musa Ahmed Bororo dake wakiltar Mubi ta Kudu shima kotu ta ce tabkama shi da laifin yin amfani da sunaye uku a takardun sa.

Kotu ta ce babu Bororo a jerin sunayen da ya muka wa hukumar zabe da a dalilin haka kotu ta tsige shi.

Kotu ta umarci hukumar zabe da ta janye satifiket din da ta mika masa ta ba Musa Dirbishi na jam’iyyar PDP.

Musa ya ce bai yarda da wannan hukunci ba, zai daukaka kara.

Share.

game da Author