Wasu gaggan ‘yan fashi da makami sun tari aradu, yayin da suka bude wa tawagar mataimakin gwamnan Jihar Nasarawa wuta, har suka kashe ‘yan sanda uku da ke tsaron lafiyar sa.
An bude wa tawagar ta Emmanuel Akabe, mataimakin gwamnan Nasarawa wuta ne jiya Talata, a lokacin da ya ke kan hanyar sa ta zuwa Abuja daga Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa.
An yi wa tawagar motocin mataimakin gwamnan kwanton bauna ne kusa da garin Akwanga, wajen karfe 6 na yammacin jiya Talata.
Kakakin Yada Labaran Rundunar ‘yan sandan Nasarawa. Usman Sama’ila ya tabbatar wa manema labarai wannan hari da ‘yan fashi suka yi wa tawagar Mataimakin Gwamnan Nasarawa.
Sai dai kuma Samaila bai yi wani karin haske dangane da harin ba, wanda har aka rasa rayukan ‘yan sanda uku.
Ya dai ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Nasarawa, Bola Longe ya ja zugar wasu zaratan ‘yan sanda zuwa wurin da aka yi kisan da kuma farmakin.
Sai dai kuma wani da ke cikin kwamba din motocin ya tabbatar da cewa ‘yan fashin sun tsere bayan sun kashe ‘yan sandan.
Ya kara da cewa bayan an bindige ‘yan sandan, an garzaya a gawarwakin su a Asibitin Kwararru na Dalhatu Araf da ke Lafiya.
Mataimakin Gwamnan dai bai ji ciwo ba, amma ya razana, shi ma je asibitin inda aka kai gawarwakin ‘yan sandan, amma bai yi wa ‘yan jarida wani jawabi ba.
Wannan hari da aka kai wa kwamba din mataimakin gwamnan ya kara nuna irin tsananin rashin tsaron da ake fama da shi a kasar nan.