Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa gwamnati za ta mayar da dazuka biyar rugagen Fulani a jihar.
Ganduje ya fadi haka ne ranar Talata da yake ganawa da manema labarai a Abuja.
Ya ce gwamnati zata yi haka ne domin killace fulani makiyaya da hana rikicin manoma da makiyaya sannan da bunkasa tattalin arzikin jihar.
Ganduje ya kuma ce gwamnati ta nada kwamiti da za ta tsara matakan da za su taimaka wajen ganin hakan ya faru.
“Kamata ya yi a fahimci cewa gina rugagen Fulani ba harkar gwamnatin tarayya ba ne, gwamnatocin jihohi ne yafi rataya a kansu da su samar da wannan rugage domin sune ke muamulada makiyaya.
“Gwamnati za ta gina makarantu, asibitoci domin makiyaya, zata gina kasuwanni da ofishin ‘yan sandan a wadannan rugage domin ganin cewa makiyayan da za su zauna a wadannan rugage sun samu walwala a wuraren zaman su.
Ya ce gwamnati za ta maida hankali matuka wajen inganta aiyukkan noma a jihar.
Idan ba a manta ba gwamnatin jihar Zamfara ta ware hekta 300 domin gina rugagen Fulani a dukka mazabu uku dake jihar.
Gwamnatin ta ce gina rugagen zai taimaka wajen kawar da kiyayyar dake tsakanin makiyaya da manoma sannan kuma za a samu bunkasar tattalin arzikin kasa da jihar gaba daya.