Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya umurci sakataren gwamnatin jihar Mustapha Inuwa da ya shirya wurin da shi gwamnan, Jami’an tsaro da Maharan za su hadu domin ganawa ta musamman, ko za a iya samun matsaya game da kawo karshen matsalar rashin tsaro a jihar.
Gwamna Masari ya yanke wannan hukuncin haka ne bayan zama da ya yi da jami’an tsaro, ranar Laraba a garin Katsina.
Sauran mutanen da suka halarci wannan taro da aka yi sun hada da Mataimakin gwama, Mannir Yakubu, kakakin majalisar dokoki na jihar Tasiu Musa Maigari, masu rikon kwaryan shugabancin kananan hukumomin jihar, sarkin Katsina Abdulmumini Kabir, jami’an tsaro da wakilan makiyaya Fulani.
Mai taimaka wa gawamnan kan harkokin yada labarai Abdu Labaran ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai a garin Katsina ranar Alhamis.
Labaran yace an gudanar da wannan zama ne domin karkato da hankulan masu ruwa da tsaki a jihar kan yadda za a iya kawo karshe hare-haren da ya ki ci yaki cinyewa.
“ Zubar da jinin mutanen da ake yi a jihar Katsina ya isa haka nan sannan lokaci ya yi da za a hada hannu gaba daya domin gaggauta kawo karshen wannan ta’addanci da ya addabi mutanen jihar.
“A shirye nake in gana da kowa da kowa domin kawo karshen matsalar tsaro a jihar Katsina.”
Masari ya ce gwamnati zata dauki zafafan matakai idan har maharan suka yi wa gwamnati kunnen uwar shegu.
“ A dalilin haka kuwa hakki ne ga kowa da kowa ya zo a hada hannu domin ci gaban jihar da kuma ganin an kawo karshen ta’addanci a jihar.