Yadda mata ta kashe mijinta don ta koma gidan tsohon mijinta a Kebbi

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta bayyana cewa ta kama wata matar aure mai suna Auta Dogo da laifin hada baki da wasu mutane biyu domin su kashe mijinta mai sun Abdullahi Shaho.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Garba Danjuma ya sanar da haka wa manema labarai a Birnin Kebbi.

Danjuma ya ce Auta ‘yar asalin kauyen Sabongari ne a karamar hukumar Badugo sannan shi mijinta Shaho na zama a kauyen Tungar Bature ne.

Ya ce Auta ta shirya a kashe mijinta ne domin ta koma gidan tsohon mijinta mai sun Idris Garba da suka rabu.

Bayan sun amince su yi haka sai ita kanta Auta da mahaifin tsohon mijinta Garba Hassan da kanen shi garban, Garba Sahabi suka shirya yadda zasu kashe Shaho domin ta iya komawa gidan tsohon mijin nata.

Masu Laifi, Hassana da Sahabi sun bayyana wa ‘yan sanda cewa lallai sune suka kashe Shaho. Sun bishi har cikin daji suka rika sararsa da adda da takobi sannan suna jibgarsa da gora da kokara har ya rasu.

Danjuma ya ce a yanzu dai Auta, Hassan da Sahabi na tsare a ofishin ‘yan sanda sannan za a kai su kotu bayan rundunar ta kammala binciken da take yi akai.

Share.

game da Author