Masu garkuwa sun sako dan majalisar jihar Kaduna dake wakiltar Zariya a majalisar dokoki jihar ranar Juma’a da yamma.
Idan ba a manta ba masu garkuwa sun yi garkuwa da dan majalisa Ibrahim Dabo a hanyar Zariya zuwa kaduna ranar juma’a.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Yakubu Sabo a takarda da ya fitar ya tabbatar da haka inda yace DPOn maraban Jos ne ya sanar da mu cewa an cinci mota babu matuki a ciki.
A takardar Sabo yace bayan sun samu wannan labari zaratan jami’an su sun fantsama domin farautar wadannan mutane da kuma ceto dan majalisar.
Sai dai kuma a daren Juma’a ne ‘yan uwan Honarabul Dabo suka sanar da sakin dan majalisar.
Sun bayyana cewa sai da aka biya makudan kudi kafin a sake shi.
Sai dai haryanzu rundunar ‘yan sanda basu ce komai game da sakin honorabul Dabo.