Farfajiyyar fina-finan Hausa ya fada cikin rudani a cikin ‘yan kwanakin nan inda jarumai ke ta fitowa suna sukan hukumar tace fina-finai na jihar Kano da shugaban ta.
Wannan matsala da farfajiyar da fada ciki kuwa ya samo aslaine tun bayan tsare Sanusi Oscar da jami’ai suka yi inda wasu ke ganin cewa siyasa ce, ba a yi masa adalci ba.
Jarumai da dama sun yi tir da wannan kamu da aka yi masa sannan kuma sun yi kira ga shi shugaban hukumar Tace fina-finai Afakallahu Na’abba ya gaggauta sa wa a saki Oscar.
Fitattun jarumai kanar su Misbahu Ahmed, Abba Almustapha, Sani Danja da dai sauransu sun fito karara suna sukar hukumar tace fina-finai ta jihar Kano sannan suna kira da a gaggauta sakin Oscar.
Misbahu ya ce ba a yi wa Osca Adalci ba sannan kuma yana gargadin Na’abba da ya gaggauta sawa a saki Oscar.
” Ina gaya maka cewa wallahi idan ka daure ni nima zan daure ka. Daure Oscar zalunci ne kuma muna kira da a sake shi.
Shima Jarumi Sani Danja kira yayi da a gaggauta sakin Oscar daga duk inda ake tsare da shi.
Me ruwan Ali Nuhu
Mutane da dama sun yi ta korafi akan wannan kanu da akayi wa Oscar inda wasu da dama ke jibanta abin ga fitaccen jarumi, Ali Nuhu.
Wasu suna cewa da hadin bakin Ali Nuhu ne aka daure Oscar. Sai dai shi Ali bai fito ya kare kansa ba ko kuma ya ce wani abu akai ba.
” Ali Nuhu dai Jarumi ne kuma fitacce ko ka ki ko ka so, sannan ba ya aiki a hukumar tace fina-finai, dan wasa ne kamar kowa, fina -finan sa suma sai ya aika da su can kafin a bashi daman haskawa. Tsakani da Allah me ya sa ake yin haka.
” Idan akwai matsala ko kuma akidar siyasa ya bambanta bai kamata arika yi wa juna Kazafi ba
” Abi duddugi aji abin da ya faru sannan a samu matsaya kamar yadda Sani Danja ya ke kira ayi.” Inji Hassana Dalhat
Suna ganin duk shiri ne na gwambatin Kano mai ci domin bibiya ta na make duk wani da ba dan APC bane.
Neman Sulhu
Jarumin dan wasan Hausa, BMB, Wato Bello Mohammed duk shi ma ya kushe wannan tsare Oscar da aka yi kira yayi ga mutane da abokanan aikin sa da su rika sara suna dubin bakin gatari.
BMB ya ce kiran sunayen wasu ana suka babu gaira babu dalili bai dace ba.
” Kamata yayi muje mu yi bincike tukunna sannan musan dalilan da ya sa aka kama Oscar. A nawa binciken, na gano cewa lallai fa akwai matsalace da aka samu da wani fiim din da Oscar ya shirya.
” A bayanin da aka yi min, an ce shi Oscar ya shirya fim ne ba tare da ya bi dokar sakin ta ba. Bai mika ta ga hukumar tantance fim ba, yayi gaban kan sa ya saki fim din. Hakan yana da ga cikin dalilan da ya sa yake tsare, kamar yadda aka sanar dani.
Sai dai kuma da dama cikin jarumai sun ce wannan ba shi bane dalilin kama Oscar ba, dalilin itace karya dokar hukumar tace fina-finai da yayi.