Wani abu dake ci wa gwamnatin Najeriya tuwo a kwarya shine yadda masu fama da Kanjamau ke kin shan magani kamar yadda ya kamata.
Tun bayan bullowar cutar gwamnati ta ke bada maganin cutar kyauta, wayar da kan mutane da a rika yin gwajin cutar a asibitoci, wayar da da kan mutane game da yin amfani da dabarun bada tazarar iyali da dai sauran su.
Burin da gwamnati ke da shi a wannan bangare shine a samu nasarar kawar da wannan cuta kafin nan da 2030 amma haka na yi wa gwamnati barazana duk da dumbin tallafi daga kungiyoyin kasashen waje da kasar ke samu tare da nata kokarin da take yi.
Rashin shan magani da wasu masu fama da cutar ke yi na da nasaba ne da matsalolin nuna wariya, rashin magunguna, rashin sani game da cutar da sauransu da ake fama da su kasar.
Dalilan da ke masu fama da cutar kin shan magani
1 – Kyamar masu fama da cutar da mutane ke yi na sa mutane su kaurace wa shan magani.
Kyamatar da ake nuna wa masu fama da wannan cuta yakan hana wasu da dama samun aikin yi, aure, zuwa karban magani a asibiti, boye magungunan da suke sha da sauran su.
A takaice dai har ma’aikatan kiwon lafiya na kyamatar su a wasu lokutta da sai mutum ya nemi gwara ma kada ya je asibitu kawai ya zauna a gida abi. Sa.
2 – Na biyu kuwa mutanen da suke dayke da cutar Kanjamau kan sadakar shikenan tasu ta kare. Ba za su sake zuwa asibiti domin magani. Hakan shima na yi wa gwamnati katanga wajen ganin aikin kawar da cutar na yin tafiyar hawainiya.
Kanjamau a Najeriya
Sakamakon binciken da hukumar hana yaduwar cutar kanjamua (NACA) da tayi, ya nuna cewa akalla mutane miliyan 1.9 ne ke dauke da cutar kanjamau a kasar nan.
Hukumar NACA da hadin gwiwar wasu kungiyoyin kiwon lafiya na Najeriya da kasashen waje sun gudanarvda bincike domin kididdigar adadin dake dauke da kanjamau, Hepatitis B da C a kasar nan.
Sakamakon binciken ya nuna cewa mutanen dake dauke da cutar kuma masu shekaru 15 zuwa 49 sun kai kashi 1.4 inda daga ciki kashi 1.9 mata ne sannan kashi 0.9 maza ne.
Bayan haka binciken ya kuma nuna cewa yankin kudu maso kudu ne ya fi yawan mutanen dake dauke da cutar a kasar nan inda yawan su ya kai kashi 3.1.
A Arewa ta tsakiya mutanen dake dauke da cutar sun kai 0.2, kudu maso gabas kashi 1.9, kudu maso yama kashi 1.1, arewa maso gabas kashi 1.1 sannan Arewa Maso Yamma kashi 0.6.
Mafita
Domin samun nasara a hana yaduwar cutar gwamnati ta yarda ta kara wa fannin kiwon lafiya kason kudi daga cikin kasafin kudi na shekara.
Gwamnati za ta inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin bada magunguna da yi wa mutanen kauyen gwajin cutar.
Bayan haka kungiyar masu fama da kanjamau na yankin Kudu maso yamma (NEPWHAN) sun yi kira ga gwamnati da ta maida hankali wajen horas da ma’aikatan kiwon lafiya kan yadda zasu rika kula da masu fama da cutar a asibiti.
Discussion about this post