El-Zakzaky ya kamo haryar dawowa Najeriya

0

Shugaban kungiyar Shi’a Ibrahim El-Zakzaky ya kamo hanyar dawowa ƙasa Najeriya daga Ƙasar Indiya.

Jirgin El-zakzaky ya baro Indiya tun da misalin karfe 5 na yammacin Alhamis.

Jagoran mabiya Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya nemi dawowa gida domin sake shirin neman magani a wata kasa, ba Indiya ba.

Malamin ya nemi dawowa Najeriya, kwana daya tal bayan isar sa kasar Indiya, inda aka shirya yi masa magani shi da matar sa Zeenat.

Sun isa asibitin ne tare da matar sa, bayan Kotun Kaduna ta bada sa domin neman magani a kasar waje.

Murna ta koma ciki bayan isar su asibitin Medanta, kamar yadda malamin ya bayyana a cikin wani faifan jawabi da ya fitar da kuma rubutacciyar wasika.

El-Zakzaky ya nemi dawowa Najeriya cikin gaggawa, domin sake shirin tafiya kasar Turkiyya, Malaysia ko wasu kasashe da suka nuna za a iya yi masa magani a can baya ga Indiya din da aka yi masa tayi tun da farko.

“Yanzu mu na birnin Delhi ne a Indiya. Kamar yadda dai aka sani an yi shiri na a zo nan domin, bidar lafiya na warkar da wasu matsaloli da muke tare da su, ni da Malama Zeenah. Ita Malama Zeenah akwai cikakken harsashi a jikinta, sannan kuma bayan haka nan akwai bukatar canjin kokon gwiwowinta guda biyu da kuma wasu matsaloli.

“Ni kuma akwai buraguzan harsasai wanda suka farfashe, ‘yan kanana a idanu na da kuma wasu a hannu na, da kuma wasu a cinya ta ta dama wadanda su ne suka rinka yin aman guba, wanda ya sabbaba matsaloli.

“Wadanda daga baya muka gano su ne suka sabbaba mini wannan shanyewar wani barin jiki, na farko da na biyu.”

El-zakzaky ya ci gaba da cewa”

“To muna tunanin abin da ya kamata a yi na farko shi ne a kwashe wadannan harsasai, wanda yin wannan aikin ba za a iya yi a gida ba, kuma likitoci suka ce a je waje inda ya kamata a yi.

Martanin gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ƙaryata saƙon sautin da Sheikh Ibrahim El-zakzaky ya fitar daga ƙasar Indiya inda ya koka kan yadda aka hana shi sakat da matarsa Zenat a asibiti.

Idan ba a manta ba, El-zakzaky ya saki saƙon sauti da ke kunshe da bayanan yadda ake muzguna masa a asibiti a Indiya.

A martani da gwamnatin Najeriya ta yi game da wannan saƙo, Najeriya ta ce babu gaskiya a cikin duka abin da El-zakzaky ya faɗi.

Grace Gekpe, babban sakatariyar ma’aikatan Yaɗa Labarai da Al’adu ta ce tun a ƙasar Dubai kafin ma su isa Indiya, El-zakzaky ya fara nuna wasu halaye da ba haka a ka shirya da shi ba.

” Na farko dai ana isa filin jirgi a Dubai, sai El-zakzaky ya nemi jami’an dake tare dashi su miƙa masa Fasfo ɗinsa. Tun daga nan aka yi ta daga dashi har aka isa ƙasar Indiya.

” Sannan kuma ina so kowa ya sani cewa El-zakzaky da kansa ya zaɓi wannan asibiti da aka kaishi tare da mai daƙin sa.

” Bayan haka kuma sai ya ce shi ba zai kwanta a asibitin ba kuma a kama masa babban Otel ya koma can ya zauna sannan a janye ƴan sandan da ke tsare shi. Anan ne fa jami’ai suka ce Bisar sa ba na yawon shaƙatawa bane, saboda haka iyakan sa Asibiti.

” Sannan ya rika tilasta wa likitocin asibitin cewa ba za su duba shi ba sai dai an turo wasu zabaɓɓun likitoci da shi ya yarda da su su duba shi. Likitocin Indiya suka ce nan ko bai isa ba ko ya tsaya a duba shi ko kuma ya koma Najeriya.

Grace ta ci gaba da cewa haka fa aka yi ta fama da El-zakzaky har wakilan gwamnatin Indiya suka ce su fa baza su yarda ya shigo ƙasar su ya nemi ƙulla wata maƙarƙashiya ba, idan neman maganin ba zai yiwu ba toh fa gaskiya ya tattara ya koma Najeriya.

Share.

game da Author