DALLA-DALLA: Yadda gogarman masu garkuwa da mutane, Wadume ya tsere a kwale-kwale

0

Wannan wani sabon binciken kwakwaf ne da PREMIUM TIMES ta gudanar, inda ta bankado harkalla, kulle-kulle da kisan-fin-karfin da sojoji suka yi wa zaratan ‘yan sanda uku, sannan suka kubutar da gogarman mai garkuwa da mutane daga hannun ‘yan sanda. Dama Hausawa na cewa “makashin ka na gindin ka.” Ku karanta ku ji yadda wannan jarida ta baje muku komai a kan faifai.

An yi wa wadannan zaratan ‘yan sanda masu zakulo masu garkuwa da mutane su uku kisan-gilla ne a daidai kauyen Gidinwaya, wanda ke tsakanin garin Ibi da Wukari a Kudancin Jihar Taraba.

Akwai shingen sojoji a kan kwalta, daidai Gidinwaya, kuma sojojin da ke tsaro da binciken motoci masu wucewa a Gidinwaya din ne suka bude musu wuta. Sojojin daga Bataliya ta 93 da ke Takum ne aka tura su domin aiki a shingen na kan kwalta.

Wannan kisan-gilla ya haifar da babbar barazana ga lamarin tsaron kasar nan tare kuma da haifar da rashin jituwa mai tsami tsakanin Sojojin Najeriya da ‘yan sandan Najeriya.

Jami’an ‘yan sandan da aka bude wa wuta sun a tafiya ne a cikin wata fatar mota bas, sun fito ne daga Ibi, inda suka kamo wani rikakken mai garkuwa da mutane mai suna Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume.

Rahoton Wakilin PREMIUM TIMES daga wurin da aka yi kisan

Wakilin PREMIUM TIMES ya ziyarci har wurin da sojoji suka kashe ‘yan sandan a Gidinwaya da ke kan titin Ibi zuwa Wukari.

Binciken da ya yi a can da za ku karanta a yanzu, har da ikirarin da mutanen kauyen suka yi, wadanda ya tattauna da su dangane da yadda abin ya faru.

Binciken PREMIUM TIMES a kauyen ya sha bamban da abin da sojohi suka bayyana cewa ya faru a kauyen na Gidinwaya.

A halin da ake ciki a yanzu, kauyen Gidinwaya kewaye ya ke da sojoji, wasu a kwak-kwance cikin shirin damarar yaki a cikin daji, tsallaken inda aka bindige ‘yan sandan. Sun sa-ido sosai su na lura da yadda mazauna kauyen ke gudanar da harkokin su.

Mutanen kauyen su kuma su na cikin tsaro da fargabar abin da zai iya samun su idan suka fai gaskiyar abin da ya faru dangane da kisan Sufeto Mark Ediale, Sajen Usman Danzumi da Sajen Dahiru Musa. Sai kuma wani farar hula mai suna Jibrin da shi ma a lokacin sojojin suka harbe su tare.

SOJOJI KO ‘YAN SANDA: Wa ya fara buɗe wuta

A sanarwar da Kakakin Yada Labarai na Sojojin Najeriya, Sagir Musa ya fitar ranar Larabar makon jiya, ya bayyana cewa sojoji sun yi tsammanin masu garkuwa da mutane ne. Kuma an tsayar da su, amma suka ki tsayawa. Sannan kuma Sagir ya ce ‘yan sandan ne suka fara bude wa sojojin wuta.

Wasu shaidu guda biyu sun tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan sandan ba su bude wa sojoji wuta ba, kamar yadda su mahukuntan sojojin suka yi ikirari.

Amma kuma shaidun sun tabbatar wa wakilin PREMIUM TIMES cewa ‘yan sandan ba su tsaya a shingen sojojin ba.

An bindige ‘yan sandan kamar mita 100 daga inda shingen sojojin ya ke.

Yadda yaran Wadume Suka riƙa bin Ƴan sanda a baya tun daga Ibi

“Wato su yaran Wadume sun rika bin motar da ‘yan sanda suke ciki dauke da ogan su tun daga Ibi, bayan da suka kamo shi daure da ankwa.” Haka wata kwakkwarar majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES, kuma majiyar ta ce a kan idon ta al’amarin da ya faru a Gidinwaya ya faru.

“Su yaran Wadume ne suka shaida wa sojojin da ke shingen bincike a nan Gidinwaya cewa farar mota bas da ke a gaban su, masu garkuwa da mutane ne suka sato Alhaji Hamisu Wadume. Dama kuma shi Hamisu Wadume din sojoji duk sun san shi farin sani, za su iya yin komai domin su kare lafiya ko ran sa.”

Majiyar ta ce daga nan ne sai sojojin suka shaida wa abokan aikin su da ke shingen kan hanya da ke daidai Gidinwaya cewa wato shinge na biyu, wadanda su din ne suka bi su, suka bindige su.

Majiyar PREMIUM TIMES ta shaida wa wakilinmu cewa farar hular da aka kashe mai suna Jibrin, wani magini ne, kuma ya ma san shi sosai. Ya ci gaba da yi wa wakilin mu karin bayanin cewa Jibrin ya na kwarmata wa ‘yan sanda masu kamo ‘yan garkuwa duk wani sirrin yadda za a kamo su.

Sannan kuma wannan majiya ta ci gaba da cewa shi Jibrin din ma yaran Hamisu Wadume sun taba kashe wani dan uwan sa.

DA DAN GARI A KAN CI GARI DA YAKI

Majiyar PREMIUM TIMES ta kara yin wani karin hasken cewa:

“To ni dai ban san dalilin da ya sa ‘yan sanda ba su tsaya a shingen sojoji ba domin a bincike su. Amma mai yiwuwa sun ki tsayawa ne saboda sun san dangantakar da ke tsakanin Hamisu wanda suka kama din da su sojojin, wanda hakan zai iya sa su kubutar da shi, su hana a tafi da shi. Saboda ya saba yi wa sojojin kyautar kudade sosai.”

Majiyar mu ta ce ta ma san daya daga cikin sojoji biyar din da suka kashe ‘yan sandan tare da Jibrin. Sai dai kuma majiyar ta ce ta yi amanna a zaton sojojin su ‘yan sandan masu garkuwa da mutane ne.

Akwai wasu mutane uku da PREMIUM TIMES ta kara zantawa da su, wadanda su ma suka hakkake cewa sojojin sun yi zaton masu garkuwa da mutane ne suka sato Hamisu Wadume za su gudu da shi. Saboda Hamisu dai mutum ne da sojojin suka sani sosai.

Kowane daga cikin su PREMIUM TIMES ta yi hira da shi ba tare da dayan ya san an tattauna da wancan ba.

Daya daga cikin majiyar PREMIUM TIMES ya tabbatar da cewa sojojin da ke shinge na biyu ne suka bi motar da ‘yan sandan ke ciki, suka rika harbin ta, har ta yi hatsari ta fadi.

“Yan sandan sun nemi fitowa su tsare, amma sai sojojin suka bude musu wuta, nan take biyu suka mutu. Shi ma Jibrin a nan ya mutu. Dan sanda na uku ya yi kokarin nuna musu katin shaidar aikin dan sanda, amma sai suka karasa kashe shi, duk kuwa da cewa sun gan shi sanye da falmara ta ‘yan sanda. Sauran ‘yan sandan kuma sun tsere, amma da harbin bindiga a jikin su, sun samu raunuka.”

JANGWANGWAMA: YADDA SOJOJI SUKA SAKI WADUME

Duk wannan kwatagwangwamar da ake yi, tuni gungun yaran Hamisu Wadume sun karaso wurin da aka harbe ‘yan sandan sun yi tsaye cikin ‘yan kallo.

“Gaba daya abin nan duk ya faru ne a cikin minti 20 kacal. Kuma duk wannan kwatagwangwama da ake tabkawa shi Hamisu Wadume ya na a kan titi zaune ya harde kafafun sa, amma daure da ankwa.

“Daga nan sai sojojin suka sa hannu suka rika ciro ‘ID card’ daga aljifan ‘yan sandan su na dubawa bayan sun kashe su kenan. amma duk da a haka sai suka rika cewa katin shaidar aikin wai na jabu ne.

NAKA SHI NE NAKA

“Daga nan sai sojojin suka rika cewa “mu tafi kawai, mu bar wurin. Sannan kuma suka rika surfa zagi su na cewa ai babu abin da ma gwamnati ke musu na kulawa, su na cewa su Wadume suka sani, domin shi ke kula da su, shi su ke cin moriyar sa.” Duk inji majiyar PREMIUM TIMES, wanda ya hakkake cewa a gaban sa aka yi komai.

“Daga nan sai sojojin suka kwance wa Wadume ankwa, suka ce ya kama gaban sa kawai, ya bar wurin. Da ido na na ga sojojin su biyar. Bayan sun cire masa ankwa, sai ya shiga wata bakar mota wadda yaran sa suka zo da ita, suka zaburi mota, suka juya suka koma hanyar Ibi.”

“Sojojin ba su ma boye abin da suka yi ba. A kan kwalta Ibi zuwa Wukari komai ya gudana. Har ma jinjina wa kan su da bajintar da suka yi suka rika yi. Ogan su ne ma mai suna Kaftin Usman ya zo ya shiga cikin su, ya karbi bindigogin ‘yan sandan yay i gaba da su.”

Wakilin PREMIUM TIMES ya gano cewa wannan jami’in soja mai suna Kaftin Usman, ya yi kaurin suna sosai a Ibi, Gidinwaya da Wukari. Duk inda ake maganar Hamisu Wadume, sai ka ji an jefo sunan sa a batun. An ce ya na alaka ta kut-da-kut tare da Hamisu Wadume.

HAMISU WADUME DA KAFTIN USMAN: ABOKIN DAMO GUZA

Wata majiyar PREMIUM TIMES ta kwatanta gogarman dan garkuwa da mutane Hamisu Wadume da Kaftin Usman cewa su biyun ‘abokan cin mushe, ba su boye wa juna wuka’.

“Komai tare su ke yi. Shi kan sa Sarkin Ibi, Aku Ibi ya na mu’amala da su. Sarkin Ibi na son sa, kowa na son sa. Wadume ya na ragargazar kudi tamkar gwamnati. Ya na biya wa mutane bukata, da warware musu matsalolin su. Na san mutane 11 da ya raba wa babura a kauyen Gidinwaya kadai.”

Majiyar mu ta yi ikirarin cewa basaraken Ibi da Kaftin Usman sun a bai wa Wadume goyon baya. Amma PREMIUM TIMES ba ta tantance wannan zargi ba.

Wasu rahotanni na nuna cewa Kaftin Usman ne ya bada umarnin a bindige sojojin. Amma dai majiyar mu da ta ce ta yi magana da abokin ta wanda soja ne a cikin wadanda sojoji biyar din da suka yi kisan, ya ce bai gamsu da wannan zargin ba.

“Duk da na san Kaftin Usman ba mutumin kwarai ba ne, na san dai abokin Wadume ne tabbas. Amma ba shi ne ya bada umarnin a kashe ‘yan sandan ba.

“Sojojin da ke shinge na farko ne suka shaida wa sojojin da ke shinge na biyu cewa ga wasu nan sun sato Wadume, don haka su tsaida su. Su kuma sojojin da ke shingen farko, yaran Wadume suka buga musu waya, su ka ce ga wasu nan sun sato Wadume.”

YADDA WADUME YA TSERE DAGA IBI

Majiya ta ce sai bayan da Bataliyar Sojoji ta 93 da ke Takum ta fahimci shirme da kasassabar da sojoji suka yi ne sannan ta tashi haikan neman yadda za su kama Wadume. Daga nan sai suka tare duk wata hanyar da ta shiga ko ta fita Ibi, har ta zuwa Wukari.

Amma majiya ta ce Hamisu Wadume ya fice daga Ibi tuni tun kafin ma sojoji su fara tare hanya. Ana jin ya fice ta cikin wuran Kogin Donga da Kogin Taraba daga Kogin Ibi. Daga nan ya shige ta Kuka cikin Jihar Filato.” Haka wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta labarta wa Kakakin Sojoji, Sagir Musa wasu bayanai da ta gano a Wukari, Ibi da kuma Gidinwaya. Amma bai ce komai ba.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Taraba, Alkasim Sanusi da kakakin su David Misal na Rundunar Taraba, sun sanar da wakilinmu cewa akwai tsatstsauran gargadin cewa kada su kuskura su yi magana da ‘yan jarida tukunna.

WAIWAYE ADON TAFIYA

Idan ba a manta ba, cikin shekarar da ta gabata ne tsohon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, T.Y Danjuma ya nuna damuwa dangane da kashe-kashen da ake yi a Jihar Taraba, har ya shawarci kowa ya tashi ya kare kan sa.

Baya cewa furucin da ya yi cewa jami’an tsaro ba su iya kare ai’ummar jihar, ya kuma yi zargin cewa wasu manyan laifukan da ake aikatawa a jihar da daurin gindin sojoji a ciki.

Wannan kakkausan zargi da ya yi dai ya janyo masa bakin jini a kasar nan, musamnan a Arewa, inda ake ganin kamar suka ce ya yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Share.

game da Author