Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Zamfara, Usman Nagogo, ya ce an karbo sama da mutane 200 wadanda mahara su ka yi garkuwa da su a wurare badan-daban a Jihar Zamfara.
Kwamishina Nagogo ya ce an karbo mutanen sama da 200 ne a cikin makonni uku da suka gabata.
Nagogo yayi wannan bayani ne a yau Litinin lokacin da ya ke taro da manema labarai a Gusau, babban birnin Jihar.
Ya ce ’yan bindigar ne da kan su suka nemi dawo da su a hannun kwamishinan, a matsayin sa na shugaban kwamitin tattauna wanzar da zaman lafiya a jihar, wanda Gwamna Bello Matawalle ya kafa kwanan baya.
Ya ce an karbo mutanen ne daga bangaren Fulani da kuma masu sintiri da aka sani da suna ‘yan sa-kai.
“Mun zauna tare da dukkan bangarorin mahara, kuma sun gane cewa nafi alfanu a gare mu baki daya har da su, shi ne zaman lafiya domin ci gaban al’umma baki daya.
“Hakan ne ya sa su da kan su suka maido wadanda suka yi garkuwa da su, sannan a na su bangare kuma su na jiran su ga gwamna ya cika musu alkawarin da ya yi na gina musu burtaloli da gandun kiwo, asibitoci da asibitocin dabbobi da kuma ruwan sha da sauran ababen more rayuwa a cikin gugagen su.
“A zaman yanzu dai dukkan bangarorin biyu su na zuwa kasuwannin da aka rufe saboda hare-hare, kuma manoma na zuwa gonakin su ba tare da fuskantar wata barazana ba.” Inji Nagogo.