KURUNKUS: Kotun Koli ta yi fatali da rokon APC na sake shari’ar zaben Zamfara

0

A yau Litinin ce Kotun Koli ta yi fatali da tankiyar nasarar zaben gwamna da aka fawwala wa jam’iyyar PDP da dukkan ‘yan takarar ta a jihar Zamfara.

Alkalai biyar na Kotun Koli a bisa jagorancin Babban Mai Shari’a Olabode Rhodes-Vivour, sun zartas da hukuncin cewa sun yi fatali da korafin da APC ta shigar inda ta nemi a sake shari’ar sabuwal ful.

Kotun Koli ta ce wannan korafi da APC ta shigar mai lamba: SC/377/2019, ba shi da wata makama ballantana tushe ko hurumin shigar da shi a kotu.

Rhodes-Vivour a madadin sauran alkalan biyar, ya bayyana cewa tuni lokacin wannan tashin-tashina ya wuce, kuma kotu ba ta da dama ko ikon sake tayar da maganar, domin bakin alkalami ya bushe.

“Kotun Koli ba za ta iya kakkabe fayil din shari’ar ta sake wata sabuwar shari’a ba. Saboda ka’ida ita ce duk wata rikita-rikitar tankiyar zaben-fidda gwani, to kamata ya yi a shigar da ita kwanaki a cikin 60 da yanke hukuncin shari’ar.”

Ya kara da cewa ganganci ne ma wani ya sake tayar da batun zaben Zamfara har ya nemi Kotun Koli da sake yin shari’ar da ita kan ta ta zartas.

“Bai yiwuwa mu zauna mu saurari karar da aka daukaka a kan hukuncin da mu ne kuma a baya muka yanke shi.” inji Rhodee-Viviour.

Tun kafin a yanke hukunci sai da lauyan APC mai suna Robert Clarke ya yi rokon Kotun Koli ta sake duba hukuncin da ta yanke a baya, domin ba a bai wa wadanda ya ke karewa cikakkar dama jin ta bakin su ba.

Share.

game da Author