Mariya Suleiman, ‘Yar shekara 19 ta caka wa wanta Sani Suleiman wuka a ciki a wajen bukin ‘Yarsu a Kano, kawai don basu samu jituwa ba wajen wakar da za a saka a wajen rawa.
Rikici ya kaure ne a tsakanin Mariya da wanta Sani bayan Sani ya nema mai saka waka a wajen bukin da da ya canja wakar da ake ji.
Ita kuma Mariya ta ce sam kada mai saka wakokin ya canja sadoda a wannan lokaci tana jin dadin wannnan waka.
A rashin jin dadin umarnin da wanta ya ba ma saka wakokin a wannan filin buki sai kawai ta dauki wuka ta caka masa.
Kafin ka ankara Sani ya fadi kasa jini na malala a kasa daga jikin sa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano Haruna Abdullahi ya tabbatar da aukuwar wannan abin tashin hankali.
” Ko da aka kira mu zuwa wannan wuri mun iske shi Sani da aka daba wa wuka kwance cikin jini.
Haruna ya ce an kama Mariya an tafi da ita caji ofis domin yin bincike bisa abinda ya faru. Sannan shi kuma Sani an garzaya dashi asibiti.
Mariya da marigayi Sani duk ‘yan gida daya ne kuma suna wajen bukin ‘Yar su ce a inda wannan tsautsayi ya faru.