A jiya Lahadi ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan yarjejeniyar sabon tsarin cinikayyar kai-tsaye a tsakanin kasashen Afrika.
Buhari ya zama cikon Shugaban Kasa na 54 daga cikin kasashen Afrika 55 da suka saka hannun amincewa da sabon tsarin.
Shugaban na Najeriya ya sa hannun ne a birnin Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, a wurin taron Shugabannin Kasashen Afrika.
Sa hannun da Buhari ya yi, ya zo ne bayan an shafe watanni da dama ya na kin amincewa ya saka hannu a kan yarjejeniyar.
Nijar wadda ke kan iyaka da Najeriya a bangaren Arewa, ita ke daukar nauyin wannan taro na musamman na 12 da Kungiyar Hadin Kan Kasashen Afrika ta shirya.
An shirya taron ne musamman a kan muhimmancin kafa wannan sabon tsari na Cinikayyar Kai-tsaye Tsakanin Kasashen Afrika, wato ‘Union on Afrikan Continental Free Trade Area’, ko kuma a takaice AfCFTA.
A can baya Buhari ya ki amincewa Najeriya ta shiga cikin tsarin, ya na mai cewa akwai bukatar a kara tuntubar masana tukunna, kafin Najeriya ta amince ta shiga cikin yarjejeniyar.
Sai dai kuma wannan jan-kafa da Buhari ya yi a baya, ya samu suka daga manyan jami’an diflomasiyyar kasa-da-kasa da kuma fitattun ’yan Najeriya, ciki har da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
Mene ne Tsarin Cinikayyar AfCFTA?
Wannan sabon tsari ne da kasashen Afrika suka rattaba wa hannu domin a samu saukin jigila da hada-hadar kayan cikin gida da ake kerawa ko sarrafawa a Afrika ba tare da gindaya sharudda, shamaki ko kakaba haraji ba.
An amince cewa za a rika safarar wadannan kayayyaki daga wannan kasa zuwa waccan, ba tare da kasashen da aka kai kayan sun neman a biya musu haraji tukunna kafin a shigar da kayan a cikin su.
A baya Buhari ya soki shirin AfCFTA, sannan ya bayyana irin na sa hangen nesan da ya ke yi wa irin cinikayyar da kuma yadda za ta kunsa.
“Hankoron da mu ke yi a fannin cinikayya tsakanin kasashen Afrika, shi ne a rika safarar kayayyakin da aka sarrafa a Afrika, ba tare da kasashen na karbar haraji a kan kayan ba.”
Sai dai kuma a cikin wannan hannu da Buhari ya sa, ba a sani ba ko an duba damuwar Najeriya akan wannan tsari.
Najeriya ta yi jinkirin sa hannu ne a kan yarjejeniyar wadda ta fara aiki a tsananin kasashen Afrika tun a ranar 30 Ga Mayu, domin ta samu damar tuntubar masana tattalin arziki da shawarwarin da kwamitin da aka kafa a kan shirin cinikayyar zai bai wa gwamnati.
A lokacin ita kuma Fadar Shugaban Kasa ta nuna cewa da zarar ta karbi rahoto daga kwamitin ta za ta rattaba hannu a kan tsarin na AfCFTA.
Najeriya ce kasa ta 53 da ta sanya hannu a kan yarjejeniyar. Amma akwai cikon ta 54, wato Jamhuriyar Benin wadda ita ma ta sa hannu jiya. Da kuma Kwamishinan Cinikayya na Kungiyar Kasashen Afrika, Albert Muchanga, ya bayyana cewa Benin za ta saka hannun amincewa a jiya Lahadi.
Kasashe 44 ne suka saka hannu a cikin watan Maris a taron da aka gudanar kasar Rwanda a birnin Kigali, cikin Maris, 2018. Yanzu dai Eritrea ce kadai ake jira ba ta kai gas a hannu ba.
Kin saka hannun da Najeriya ta yi tun da farko, a matsayin ta na kasa mafi karfin tattalin arziki a Afrika, ya haifar da damuwa a fadin Nahiyar Afrika da kuma kasashen duniya.
Harkokin cinikayya a kasashen Afrika ya na tafiyar hawainiya, domin kashi 17 bisa 100 ne kacal na kayan da ake sarrafawa a Afrika ake sayar da su a cikin kasashen Afrika din.
Amma kuma kamar yadda wani bayanin da ‘Foresight Africa’ ya wallafa, an nuna cewa kashi 69 na kayan ana fitar da su ne kasashen Turai, 59 cikin 100 kuma zuwa kasashen Asiya. Cibiyar Nazarin Hada-hadar Kudade da Cinikayya ta Brookings ce ta wallafa bayanan cikin wannan shekarar.
Ana ganin tunda kasashe irin su Najeriya, Afrika ta Kudu da Masar sun shiga cikin yarjejeniyar gadan-gadan, to cinikakka tsakanin kasashen Afrika zai matukar karuwa, a cikin wannan nahiya wadda ke da karfin arziki kusa naira dala tiriliyan 2.5.
Alfanun Tsarin Cinikayyar Kasashen Afrika (AfCFTA)
Jiya Lahadi ne Shugabannin Kasashen Afrika suka hadu a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, suka kaddamar da Sabon Tsarin Cinikayyar Kasashen Afrika, wanda za a rika safarar kayayyakin da kasashen ke sarrafawa a tsakanin kasashen na Afrika, ba tare da ana biya musu harajin shigar da su wannan kasa daga waccan ba.
An yi hasashen wannan sabon tsari zai hada kan harkokin cinikayya da kasuwancin sama da mutane bilyan 1.3 a fadin nahiyar, sannan kuma zai samar da habbakar tattalin arziki har na kimanin dala tiriliyan 3.4. Hakan ake jaddada cewa zai kawo wani sabon sauyin kawo ci gaban nahirar baki daya.
Shekaru hude kenan ana ta hakilon kafa tsarin tare da neman kaddamar da shi. Har dai ta kai a yanzu an kaddamar da shi a Yamai, ta Jmahuriyar Nijar, a Jiya Lahadi.
Wannan tsari wanda shi ne mafi girma tun bayan kafa Kungiyar Cinikayya ta Duniya, wato ‘World Trade Organisation’ a cikin 1994. Zai bude kofofin kawo ci gaban tattalin arzikin kasashen Afrika, wanda ya dade a tsaye cak, tsawon shekara da shekaru.
“Yanzu dai idanun duniya zai juyo zuwa Afrika,” inji Shugaban Masar, Abdel Fattah al-Sisi, a lokacin da ya ke jawabi a wurin taron jiya Lahadi a Yamai.
Kaffa-Kaffar da Najeriya ke yi wa Tsarin AfCFTA
Duk da cewa karfin Najeriya ya fi dogara ne kacokan a kan fitar da danyen man fetur a bangaren samun kusan kashi 90 bisa 100 na kudaden shigar da gwamnatin tarayya ke takama, Najeriya na kaffa-kaffa da shirin ne saboda tsoron kada a rika yin ambaliyar kayayyaki masu karancin farashi a cikin kasar daga kasashen Afrika.
Wannan kuwa idan har ta faru, to dakile kokarin da ake yi na farfado da kananan masana’antun cikin kasar wadanda suka durkushe, tare kuma da sacce tayoyin kokarin inganta fadada noma da kasar ke yi.
Wannan tsari kuwa zai bai wa Afrika ta Kudu damar shigar da kayayyakin ta cikin kasashen Afrika, a matsayin ta na kasa mai sarrafa kayayyakin da idan su ka shiga kasuwannin Afrika, tilas su samu nasibi.
Masar da Afrika ta Kudu da Najeriya su ne mafi karfin tattalin arzikin Afrika da kaso kusan 50 bisa 100 na karfin tattalin arzikin nahiyar.
Discussion about this post