Ma’aikatan ‘N-Power’ 500 sun ajiye aiki a Zamfara

0

Akalla ma’aikatan tsarin tallafin N-Power su 500 suka ajiye aikin a Jihar Zamfara bayan sun samun aikin dindindin.

Shugaban Hukumar SIP na Jihar Zamfara Kabiru Umar ne ya bayyana haka.

Umar ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Gusau, babban birnin Jihar a yau Talata.

Ya ce wadanda suka ajiye ayyukan na su sun samu aiki ne a karkashin gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jiha da wasu hukumomi daban-daban.

Ya ce an dauki ma’aikatan N-Power har 11,122 tsakanin 2016 zuwa 2017 a jihar Zamfara. An dauke su ne a bangarorin ayyuakan lafiya da noma.

Umar ya kara da bayyana cewa wasu ma’aikatan sa-kai su 321 ma an dauke su a karkashin N-Power, inda suka yi ayyukan na’urorin kwamfuta da sauran fasahohin da suka danganci zamani.

Sai dai kuma ya yi tsokacin cewa saboda rashin wadatattun motoci, akwai matsala sosai wajen yadda za a iya bi gari-gari ana yin duba-garin ayyukan wadannan masu ayyukan sa-kai a karkashin N-Power din.

“ Mu na ci gaba da samun korafe-korafe daga wasu shugabannin makarantun firamare da na Sakandare cewa wasu ma’aikatan na N-Power su na fashin zuwa makarantu koyarwa. To amma babu yadda za mu yi, saboda mu na fama da karancin motocin zirga-zirgar da za mu iya zuwa duba-gari.”

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin jihar Zamfara ta taimaka musu da motocin zirga-zirgar gudanar da ayyukan su, ciki har da zagayen duba-garin ma’aikatan su.

Share.

game da Author