Shugaban Kasa Mauhammadu Buhari ya bayyana cewa lallai fa da an mika wa Abiola mulkin Kasarnan a 1993, da yanzu ba a fama da matsalolin kabilanci a Najeriya.
Buhari ya fadi haka ne da yake karbar bakuntar wasu shugabannin Yarbawa daga jihar Ogun a fadar gwamnati dake Abuja.
” Da ace an mika wa Abiola mulkin Najeriya a wancan Lokaci da ba a fama da matsalolin rikice-rikice na addini da Kabilanci a kasar nan kamar yadda ake ta kokuwa da su yanzu. Abiola daga Yankin Yarbawa ya fito sannan ya zabi mutumin Barno, kuma Kanuri dan Arewa a matsayin mataimakin sa kuma dukkan su musulmai suka karade kasar nan kaf sannan mutane gaba daya suka amsheshi.
” Yayi amfani da karfinsa da dukiyarsa wajen tabbatar da ganin Najeriya na daure tamau wuri daya. Sannan kuma na saka wa filin wasa na Abuja sunan Abiola domin nan gaba matasa masu tasowa zasu rika yin Tambayoyi domin neman sani.
A karshe Shugaba Buhari ya yabawa tawagar tare da gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun kan wannnan ziyara da suka kawo masa.
A nasu barayin, jagoran tafiyar, Gwamna Abiodun ya shaida wa jinjina wa shugaba Buhari kan girmamawa da yayi wa marigayi Abiola a lokacin mulkinsa. Bayannan ya roki shugaban kasa da ya maida hankali wajen samar da ababen More rayuwa a yankunan Kudu Maso Yamma, ta hanyar gina manyan tituna da gyara su da kuma kasa baki daya.