Uwar Jam’iyyar PDP ta Kasa ta nemi Majalisar Dattawa ta gaggauta mika sunayen sabbin minitocin da Shugaba Muhammadu ya damka mata a hannun EFCC.
Kakakin Yada Labarai na EFCC, Kola Ologbodiyan ne ya bayyana haka a cikin takardar manema labarai da ya fitar jiya Litinin.
Ya ce idan ana son a tantance nagari daga cikin mugu, to ya zama wajibi a damka sunayen sabbin ministocin gaba dayan su, domin EFCC ta yi musu binciken kwakwaf.
PDP ta ce, “a cikin sunayen sabbin ministocin, akwai tsoffin gwamnoni wadanda suka saci kudi, suka yi wa jihar su karkaf. Kuma akwai tsoffin ministoci wadanda suka jide kudaden ma’aikatun da suka yi aiki. Da yawan su akwai ‘kaulasan’ din da EFCC ta rataya a wuyan su.”
PDP ta ce akwai mamaki sosai ganin yadda sunayen wasu tantiran tsoffin gwamnoni da tsoffin ministoci suka fito cikin sabbin ministocin Buhari.
Sanarwar ta ce wannan ya nuna cewa Buhari ya saki layin yaki da cin hanci da rashawa, ya koma ya na jaddada cin hanci da rashawa.
“Dama ya ce ba zai nada kowa minista ba sai wanda ya sani gar-da-gar. To ya nuna wa duniya irin mutanen da shi ya dauka nagartattu, wadanda ya sani gar-da-gar.”
PDP ta ce yanzu duniya ta ga wadanda Buhari ya ce ya sani kuma nagartattu a ta sa fassarar.
Sanarwar ta kara cewa dukkan wadanda ake zargin nan kuma wadanda Buhari ya zaba a matsayin sabbin ministoci sun kasa kare kan su daga zargin satar kudaden kasar nan da na jihohin su.
“Ku dubi yadda ya sake mika sunan wani tsohon minista da aka samu dumu-dumu cikin harkallar kwangilar naira bilyan 2.5 ta hukumar NBC.”
A karshe PDP ta ce iska ya hankada labulen Buhari, an fahimci yadda gwamnatin sa ke daure wa cin hanci da rashawa gindi, sabanin romon-kunnen da ya yi wa al’ummar kasar nan a 2015, ya ce zai magance rashawa da cin hanci idan ya hau mulki.
Discussion about this post