Majalisar dokokin jihar Kaduna ta ki amincewa da sunan Abubakar Aliyu da gwamnan jihar Kaduna ya aika da shi a yi masa kwamishinan Ayyukan Gona jihar.
Babban dalilin da yasa Aliyu bai shallake wannan siradi ba kuwa shine wai don a shekarun baya ya taba ci wa gwamna Nasir El-Rufai fuska bisa wasu manufofin sa da ayyuka da yayi a Kaduna.
Dan majalisa Tanimu Musa wanda shine kakakin kakakin yada labarai na majalisar, ya bayyana ruwa ne ya hadiya Aliyu bai shirya ba.
Shima kakakin majalisar Aminu Shagali ya ce sun ki amincewa da Aliyu Abubakar ne sabo ya rika zagin manufofi da ayyukan gwamna El-Rufai a shafukan sa a 2017.
” A lokacin da El-Rufai ya kori malaman makaranta a Kaduna, Aliyu ne kan gaba wajen ci masa mutunci, inda ya rika rubutawa a shafin sa na Facebook cewa wannan kokari na El-Rufai da daidai bane, wai muzguna wa talakawa ne. Sannan kuma ya rika caccakar El-Rufai kan matsalolin tsaro da ya addabi jihar a wancan lokaci.
” Ya manta cewa ashe komai daren dadewa wata rana sai ya lashe aman sa. Gashi nan yanzu a gaban mu kiri-kiri kuma ba zamu amince masa ba ya zama kwamishina a jihar. Duk wanda yaci tuwo da mu miyar ma ba a kada ta ba. Ba dai ya zagi Gwamna El-Rufai ba shima ya dandana yanzu.
” Ya dade yana zagin wannan gwamnati meya sa yanzu kuma yake so yayi aiki a gwamnatin.