Kotu ta ce Hukumar Kwastan ta biya kamfanin Maggpiy diyyar naira bilyan 5.5

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke hukuncin tarar naira bilyan 5.5 a kan Hukumar Kwastan ta Kasa da Shugaban Hukumar Gudanarwar Kwastan, bisa dalilin kwace kwantina 90 mai dauke da shinkafa mallakar kamfanin Maggpiy Tarading TFZE.

A cikin karar da Maggpiy ya shigar mai lamba FHC/CA/CS/40/2017, ya bayyana cewa jami’an Kwastan sun kulle rumbun ajiyar kayan sa da ke Yankin ‘Free Trade Zone’ a Calabar, a ranar 18 Ga Maris, 2017.

Kamfanin ya ce an kulle masa ma’ajiyar kayayyakin a lokacin da ya ke makare da kwantinoni da ke kulle da shinkafa a ciki.

Kamfanin Maggpiy ya kara da cewa baya ga kulle masa sito din na ajiya da kwastan suka yi, wasu jami’an kwastan din sun saci shinkafa mai tarin yawan gaske.

Sannan kuma jami’an kwastan din sun kama wasu tireloli 40 a kan hanyar Onne zuwa Fatakwal, wadanda ke dauke da shinkafar da aka yi niyyar kaiwa a Tinapa. Sun tsare motocin tsawon kwanaki 120 ba tare da wasu hujjojin da dokar Najeriya ta gindaya ba.

Da ya ke yanke hukunci a jiya Laraba, Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya bayyana cewa Hukumar Kwastan da kuma Shugaban Hukumar Gudanarwar Kwastan duk sun aikata abin da doka ba ta ce su aikata ba.

Mai Shari’a ya yi watsi da hujjojin da lauyoyin hukumar kwastan da na shugaban hukumar gudanarwar kwastan suka gabatar a matsayin dalilan kulle sito din da kuma rike motocin masu dauke da shinkafa.

Sun ce sun rike kayan ne a karkashin dokar Ka’idojin Shigo da Kayayyaki ta Ma’aikatar Harkokin Kudade. Mai Shari’a dai bai gansu da wannan bayani ba.

Mai Shari’a ya ce takardar suka gabatar a matsayin dalilin rike shinkafar, ba ta da wani bambanci da katardar jaridar da ta yi kwantai, domin babu wanda ya sa mata hannu. Sannan kuma dokar da su ke tinkaho da ita a karkashin Ma’aikatar Harkokin Kudade, ba ta shafi kayan da ke a ‘Free Trade Zone’ ba.

Sannan kuma Mai Shari’a ya ki yarda da takardun umarni da Kwastan suka gabatar masa na kama kayan. Ya ce takardun da kwastan suka gabatar akwai rainin hankali tare da su, saboda sai bayan da aka kama kayan a ranar 18 Ga Maris, 2017 da kwanaki da yawa sannan aka buga ko aka rubuta umarnin.

Sannan kuma ya kara da cewa dukkan bayanan da ke kunshe cikin takardar umarnin kama kayan, babu dokar da ta bayar da ikon yin yin haka din.

Mai Shari’a ya ce an kama kaya ranar 18 Ga Maris, amma kuma an buga takardar halascin kama kaya a ranar 30 Ga Maris duk a cikin 2017.

Yadda Kwastam suka sace buhunan shinkafa 2,160

Mai Shari’a ya yi matukar nuna rashin jin dadin yadda bayan an bude sito din, aka gano cewa jami’an Kwastan sun dirka satar dubban buhunnan shinkafa.

“Yayin da aka zo ana kirga yawan shinkafar da ke cikin sito-sito din bayan an bude su, Mai Shari’a ya gamsu da cewa an jidi buhuna 19,421 na babban buhun shinkafa mai 50kg. Sai kuma buhuna 1,639 na karamin buhun shinkafa mai nauyin 25kg.

“Wadan da ake zargi sun kasa kare kan su daga bacewar wadannan tulin buhunnan shinkafa a gaban kotu.

Sannan kuma ya ce baya ga dirka sace wa kamfanin shinkafa da kwastan suka yi, sun kasa gabatar da hujjar cewa shinkafar ta sumogal ce.

Har ila yau, Mai Shari’a ya nuna rashin jin dadin yadda jami’an kwastan suka ki bin umarnin kotu har sau biyu a baya.

A can baya dai kotu ta bayar da umarni a saki kayan. Kin bin umarnin kotun ne ya sa har da yawan shinkafar ta lalace aka yi asara, saboda dadewar da ta yi a kulle.

Bayan Mai Shari’a ya ci Kwastan tarar biyan kamfanin diyyar naira bilyan 5.5, sai kuma ya gargadi kwastan da kada su kara zuwa yankin ‘Free Trade Zone’ su na kama kayan mutane, domin a cikin Najeriya ne yankin yake.

Share.

game da Author