ZABEN 2019: Sharwarwari 21 kadai za a iya amfani da su daga Kungiyoyin Kasashen Waje -INEC

0

Shugaban Hukumar Zabe, Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa daga cikin shawarwari 69 da jami’an kasashen waje suka bayar domin inganta zabe, 21 ne kawai za a iya aiwatarwa a kasar nan.

Ya bayyana hakan ne kuwa a ranar Litinin, lokacin da ya ke jawabi wurin taron bita da nazari da bin diddigin yadda zaben 2019 ya gudana.

INEC na ci gaba da gudanar da irin wannan taro domin samun shawarwari da nazarin inda ya kamata a kara kokari da kuma inda aka samu matsaloli wajen gudanar da zabukan 2019.
Yakubu ya ce kusan dukkan shawarwarin da aka bayar za su iya yiwuwa a aiwatar da su, amma fa har sai idan an yi wa Dokar Zabe kwaskwarima tukunna.

Ya ce wannan kuma aiki na Majalisar Tarayya.

Da yawa daga cikin wadannan kungiyoyi sun bayar da shawarwarin yadda za a inganta zabe.

Kungiyar Tarayyar Turai ta gabatar da shawarwari 30, CW kuma 24 yayin da NDI/IR1 suka hadu suka gabatar da shawarwari 15.

INEC ta ce shawarwari 9 ne kadai daga cikin 30 na EU za a iya amfani da su a yanzu. Sai kuma 8 daga CW sai kuma 4 daga NDI/IRI.

Yakubu ya ce sau da yawa batu ko sha’ani na yi wa dokar zabe kwaskwarima, ba aikin INEC ba ne. “Tilas sai dai mu garzaya Majalisar Tarayya.”

A karshe ya ce za a fara amfani da wasu shawarwarin a zaben gwamna na jihohin Bayelsa da Kogi a ranar 16 Ga Nuwamba da kuma zaben cike-gurbin dan majalisa daya da za a yi a ranar 3 Ga Agusta, 2019 a Jihar Filato.

Share.

game da Author