Rundunar tsaro na NSCDC ta sallami daya daga cikin ma’aikacinta mai suna Innocent Oshemi a dalilin kashe mutane biyu da ya yi.
Jami’in rundunar Abdullahi Gana ya sanar da haka a wata takarda daya rabawa manema labarai a Abuja ranar Laraba.
Gana ya ce Oshemi ya harbe Mamman Wuya ma’aikacin rundunar dake aiki a bakin ruwa a jihar Legas (LADOL) da wani ma’aikacin kamfanin ‘Samsung Heavy Industries) kuma dan kasar Korea Tea Kun ranar 8 ga watan Afrilu 2019.
“Da muka samu labarin abin da Oshemi ya aikata sai muka kafa kwamiti domin yin bincike akai, daga nan sai muka gano cewa lallai ya aikata hakan, bayan na’urar daukar hoto da bidiyo ya dauko shi a daidai lokacin da yake aikata kisan.
“A yanzu dai Oshemi na tsare a hannun ‘yan sandan domin ci gaba da bincike.
Bayan haka Gana ya karyata zancen bashin kudade da Oshemi ke bin rundunar.
“Oshemi baya bin mu bashi sannan ba ma biyan ma’aikatan mu albashi da alawowinsu da tsabar kudi domin hukumar IPPIS da muka yi rajista da ita ne ke biyan ma’aikata a banki.
A karshe Gana ya yi takaicin faruwan wannan mummunar abu sannan ya ce rundunar ta dauki mataki domin ganin irin haka bai sake faruwa ba.