Shugaban Hukumar Hana Fasa-kwauri ta Kasa, Hamid Ali, ya ce Kwastan sun kone kwantina 58 ta Tramadol da sauran muggan kwayoyi har na naira bilyan 14 da milyan 700,000.
Ya ce an kone magungunan ne a karkashin Kwamitin Kwastan na Kone Muggan Kwatoyi tare da hadin guiwar sauran hukumomin hana safara da tu’ammali da muggan kwayoyi.
Ya ce an kone su ne a a bannan sansanin jibgewa da kone muggan kwayoyi na cikin dajin Shagamu a Jihar Ogun.
Da ya ke jawabi a yayin kone muggan kwayoyin, Hamid Ali wanda Mataimakin sa Kathleen Ekekezie ta wakilta, ta yaba wa irin kokarin da sauran hukumomin irin su NAFDAC da NDLEA me yi wajen dakile muggan kwayoyi a kasar nan.
Ya ce jajirtaccen aikin hana shigo da kwayoyi da Kwastan ke yi da kuma hana tu’ammali da ita da NDLEA da NAFDAC ke yi, aiki ne na ceto rayuwar al’umma da kuma sadaukar da kai saboda su.
Ya yi kira da daukacin jama’a a fadin sasaan kasar nan, su rika fallasawa tare da kai rahoton masu fasa-kwaurin muggan kwayoyi a cikin kasar nan.
Sannan kuma ya roki kafafen yada labarai da dukkan ‘yan jarida su ci gaba da rika wayar wa al’umma kai dangane da illolin muggan kwayoyi.
A na sa jawabin, Shugaban Kwamitin Kone Muggan Kwayoyi, Mataimakin Kwanturola Janar, Aminu Dahiru, ya ce wadanda aka kone a Shagamu somin-tabi ne. Akwai saura da za a kone a shiyyar ofishin kwastan a Kaduna, Fatakwal da Bauchi.
A karshe ya yi nuni da cewa kafin su cimma wannan nasara ta kamen muggan kwayoyi, jami’an su sun fuskanci barazana, hare-hare, dukan-rubdugu har ma kisa.