Dan takarar shugaba kasa a zaben watan Maris, 2019, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sanarwar da Amurka ta bayar, wadda ta haramta wa wasu masu rike da mukaman siyasa shiga kasar daga Najeriya, tabbaci ne cewa an tafka masa magudi a lokacin zabe.
Atiku, wanda ya yi Mataimakin Shugaban Kasa tsakanin 1999 zuwa 2007, ya bayyana haka ne ta bakin Kakakin Yada Labaran sa, Paul Ibe a jiya Laraba.
Cikin sanarwar da ya fitar, ya ce ganin yadda Amurka da kan ta ta kyamaci rawar da wasu suka taka a lokacin zaben, wannan wata shaida ce mai nuna cewa da magudi APC ta yi nasara.
Amurka dai ba ta bayyana sunayen wadanda ta ce ta hana shiga kasar ta ba. Dokar kasar ta hana ta bayyana sunayen irin wadannan mutane, amma dai dukkan su za su san cewa an haramta musu shiga kasar.
Ta ce ta hana su sake shiga Amurka saboda haushin rawar da suka taka a yunkurin dakile turbar dimokradiyya a lokacin zaben 2019. Jama’a da dama na ganin cewa Amurka ta ware wadanda ake zargi ne da tayar da rikice-rikice a lokutan zabe.
INEC ta maida wa Atiku Martani
Sai dai kuma tun a jiya Laraba din Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta maida wa Atiku martani cewa kamata ya yi ya daina magana har ya jira sakamakon hukuncin kotu tukunna.
Kakakin INEC Festus Okoye, ya shaida wa kafafen yada labarai cewa Atiku ba shi da hurumin yin magana a kan zabe, tunda ya rigaya ya shigar da kara kotu.
Don haka a ta bakin Okoye, Atiku ya daina azarbabin yin wani fashin-bakin maganganun da suka shafi zabe, har sai kotu ta yanke hukunci tukunna.
Atiku da PDP su na kalubalantar nasarar Shugaba Muhamadu Buhari da APC a zaben shugaban kasa. Ana ci gaba da zaman shari’a a Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa, a Abuja.
Okoye ya kara da cewa, ” Tunda Shari’a ta na kotu har ma Atiku ya kammala gabatar da shaidun sa a kotu, to ba daidai ba ne ya fito a gefe ya na maganganu a kan zabe ba. Ya jira hukuncin da kotu za ta yanke tukunna.”