Majalisar Tarayya za ta binciki ayyukan da aka ki kammalawa tun daga 1999

0

Majalisar Tarayya ta yanke shawarar cewa za ta kafa gagarimin kwamitin da zai binciki dukkan ayyukan raya kasa na Gwamnatin Tarayya da aka fara amma ba a karasa ba, tun daga 1999 har zuwa yau.

Hon Francis Uduyok ne ya gabatar da wannan kudiri a zaman majalisa na jiya Labara, wanda Mataimakin Shugaban Majalisa, Idris Wase ya shugabanta.

Da ya ke gabatar da kudirin, wanda wasu su ka kara goyon baya, Uduyuk ya nuna rashin jin dadi da bacin rai ganin yadda gwamnatin tarayya ke bayar da kwangiloli alhali da yawan su ba a kammala su, tun daga 1999 har zuwa yanzu.

Dan Majalisar ya ce akwai ayyukan raya kasa sama 20,000 wadanda an biya akalla kashi 50 bisa 100 na kudin da sun haura bilyoyin nairori tun kafin ma a fara ayyukan.

Ya ce akwai ayyukan raya kasa da aka ki kammalawa a cikin kasar nan masukar muhimmanci da suka hada madatsun ruwa, asibitoci, gine-gine, gadoji, masana’antun karafa da titina masu yawa.

“Kwangila gina titin Eastwest Road tun cikin 2006 aka bada aikin, amma har yau sama da shekaru goma ba a kammala aikin ta ba.”

Majalisa ta kuma nuna damuwa a kan wadannan ayyukan da aka ki kammalawa tare da yin nunin cewa sun kawo wa tattalin arziki cikas, domin a yanzu kudin kammala su ya rufanya nunkin-ba-nunki.

Sannan kuma sun nuna cewa yanzu a kasar nan kin kammala aiki ya zama al’ada, wadda tilas idan ana son kasar nan ta ci gaba, to sai an hana wannan mummunan al’ada.

Wani abin damuwa da majalisa ta kara nunawa kuma shi ne yadda batagari manya da kanana suka mamaye wadannan gine-gine da aka yi watsi da su, suka maida su mabuyar su, kuma wuraren da suke tabka barnar cutar da jama’a da kasa baki daya.

Daga nan sai aka zartas da cewa za a kafa kwamiti wanda zai kammala binciken sa cikin watanni uku kacal.

Share.

game da Author