Doka ta bai wa INEC ikon rage jam’iyyu daga 91 zuwa 7 -Lauya

0

Wani fitaccen lauya masanin dokokin Najeriya, ya bayyana cewa Hukumar ZABE Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta na da ikon da doka ta ba ta na karfin soke rajistar jam’iyyun siyasa.

Realwan Okpanachi ya bayyana haka a cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai jiya Alhamis a Abuja.

Lauyan ya na maida martani ne dangane da wata magana da aka danganta da Kwamishinan Tarayya na Zabe Mai Kula da Jihohin Nasarawa, Kogi da Kwara, Mohammed Haruna ya yi, inda ya ce INEC ba ta da karfin ikon soke rajistar jam’iyyun siyasa.

Okpanachi ya shaida wa manema labarai cewa kafi yawan tulin jam’iyyu su kai 60 a zokacin zaben 2011, ai sai da Majalisa ta yi wa Dokar Zabe ta 2010 gyara tukunna.

Daga nan sai ya ce wannan gyara da aka yi ya bai wa INEC hurumi da dama da ikon soke duk wata jam’iyyar da ba ta ci kowane zabe ko daya ba.

Ya ce ta hanyar yi wa Sashe na 225 gyara, hakan ya bai wa INEC karfin ikon duk soke duk wata jam’iyyar da ba ta tabuka komai a lokacin zabe ba.

Daga cikin sharuddan da ya gatabar na dalilin da zai sa INEC ta soke jam’iyya, akwai: Idan jam’iyya ta kasa samun ko da kashi 25 bisa 100 na kuri’un da aka jefa a wata jiha a zaben shugaban kasa. Ko kuma kashi 25 daga yawan kuri’un da aka jefa a wata karamar hukuma a zaben gwamna.

“Idan jam’iyya ta kasa cin zaben ko da mazaba daya a zaben shugaban karamar hukuma, ko kuma ta kasa cin dan majalisar jiha ko da guda daya, ko kuma ta kasa cin kujerar ko da kansila daya, to INEC za ta iya soke wannan jam’iyyar.” Inji Okpanacha.

Daga nan sai ya yi kira da gaggawa ga INEC ta fara soke rajistar duk wasu tarkacen jam’iyyun siyasar da ba su tabuka komai a zaben 2019 ba.

Okpanacha ya kira wadannan jam’iyyu ‘yan neman kudi, ba ‘yan siyasa ba.

A karshe ya ce idan INEC ta bi diddigin yadda zaben 2019 ya gudana, to ta na da karfin ikon soke jam’iyyu daga 91 zuwa 7 kacal.

Share.

game da Author