Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya nada tsohon kwamishinan Kasafin kudin da tsare-tsare na jihar, Muhammed Abdullahi, (Dattijo) shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar.
Ga sauran nade-naden da El-Rufai yayi
1. Muhammad Sani Abdullahi- Shugaban Ma’aikatan fadar gwamnati
2. Bala Yunusa Mohammed – Mataimakin shugaban fadar gwamnati
3. Hamza Abubakar- Babban Sakataren SPHCDA
4. Ben Kure – Maitaimakawa gwamna kan harkokin Siyasa
5. Dr. Omano Edigheji- Mai taimakawa gwamna kan Bincike da Adana.
6. Maimuna Abubakar Zakari- Babban Sakatariyar Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar.
7. Dr. Habiba Ibrahim Mohammed, Miataimakawa Kan Tsare-tsaren bayanan na taswirar kasa na jihar.
8. Jamilu Albani- Darekta Janar din ma’aikatan harkokin addini
Discussion about this post