Jiya Alhamis ne aka gurfanar da Alfa Habeebulah Abdulrahman a gaban alkali, bayan kama shi da aka yi ya yi wa yarinya ‘yar shekara 16 fyade.
An gurganar da shi ne Kotun Majistare ta Ede da ke Jihar Osun.
Dama tun a ranar Litinin ne ‘yan sanda suka kama shi, sannan suka tsare shi sahen bincike na CID.
A cikin wani rahoto na musamman dai PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Alfa Abdulrahman da aka fi sani da Al-Edewy ya yi wa dalibar Islamiyyar sa fyade a garin Ede, Jihar Osun.
Yayin da Alfa Al-Edewy bai yi tantamar kwanciya da yarinyar ba, sai dai kua ya jajirce cewa ya aure ta tun kafin ya kwanta da ita a karo na farko.
Sai dai kuma malamin ya kasa gabatar da kowace irin shaida, domin iyayen yarinyar da ita yarinyar kan ta, duk sun karyata zancen aure a tsakanin sa da ita.
“Bayan kwana bakwai na shiga makarantar sa, sai ya ce na aure shi mana. Amma sai na ce masa ai auren zai shafi karatu na. Kuma ni ko ma da aure ne, ai ya yi min tsufa. Haka wadda ya yi wa fyaden ta shaida wa PREMIUM TIMES.
An gurfanar da shi a kotu, amma an bayar da belin sa a bisa ka’idar cewa sai ya cika sharuddan beli, wanda ya hada da mai belin ya zama ma’aikacin gwamnati mai mataki na 12, kuma ya kasance ya na da gidan kan sa, ba mazaunin gidan haya ba ne.
Tuni dai aka karbi belin sa tun jiya Alhamis.
Yayin da za a ci gaba da shari’a cikin watan Agusta, PREMIUM TIMES ta gano cewa iyalan Alfa din sun a ta matsa-lamba ga iyayen yarinyar su dubi girman Allah a sasanta maganar.