WUTAN LANTARKI: Shin Sayarwa ‘Yan Kasuwa Da Wutan Lantarki (NEPA) Ya Biya Kudin Sabulu? Daga Kais Sallau

0

Matsalar wutan lantarki abu ne wanda ‘yan Najeriya suka dade suna fama dashi. Gwamnatoci daban-daban sun kashe makuden kudade da sunan inganta wutan lantarki (NEPA) a Najeriya, amma abu yaci tura, ba abin da ya canja.

Matsalar wutan lantarki ya samo asali daga sakarci irin na gwamnati Najeriya. Kudaden da gwamnati Najeriya suka cire a zango na hudu na mulkin farin hulla (Fourth Republic – 1999-till_date) ya kai ace an fita daga matsalar wutan lantarki a Najeriya. Domin akwai wata gwamnati da dalan Amurka biliyon goma sha shida ($16b) ta ware domin inganta wutar lantarkin, amma ba abinda ya canja. Saboda duk lokacin da aka cire wannan kudaden da aka ware domin gyaran wutan sai wadansu tsiraru suyi awon gaba da kudaden, hakan yasa har yanzun baa samu biyan bukata ba. Idan ana amfani da wannan kudaden yadda ya dace, to ba shakka da wutan lantarki ya inganta a kasan nan.

Kais Daud Sallau

Kais Daud Sallau

Bayan duk kudaden da gwamnati suka yi ta kashewa amma baa samu biyan bukata ba sai tsahon shuganan kasa Goodluck Jonathan ya yanke shawaran sayar da wutan lantarki (NEPA) ma ‘yan kasuwa. Amma sai akasa siyasa a wannan lokacin, ba a sayarwa mutanen da suka dace a sayarwa ba. Kawai idan kana tare da gwamnati a lokacin, kuma kai mai fada aji ne, to kana cikin wadanda zaa sayarwa. Shiyasa wadanda aka sayarwa da wutan basu damu da su inganta wutan ba saboda biyan bukatarsu.

Abin dubawa a nan shine;

1 – Shin Sayar Da Wutan Lantarkin (NEPA) Kwalliya Ya Biya Kudin Sabulu?*

Ba shakka zamu iya cewa kwalliya bata biya kudin sabulu ba saboda har yanzun ‘yan Nageriya na fama da matsalar wutan lantarki (NEPA) sakamakon wadanda aka sayar musu da wutan lantarki basu shiryawa wannan harkan ba. Kawai su abinda suka sani su karba kudi idan wata ta kare, saide su ba ma’aikatan su yawan kudin da suke bukata a samo a wata (Monthly Targets). Amma basu san idan wuta ya lalace su gyara ba, basu san yadda ake sayan transformers ba, da sauran matsaloli wutan. Kawai idan wutanku ya lalace saide suce ‘yan unguwa su hada kudi kafin a kyara musu. Idan ma basu gaya muku ku hada kudi ba, to da kanku zaku hada kudin domin ko shekara goma zaayi baza su kyara ba.

Wai ace har yanzun a Najeriya idan akayi ruwan sama a yankin ku, musamman ruwa mai iska, shikenan ku baza ku samu wuta ba sai anyi gyare-gyare, idan za’ayi kwana biyar ana ruwan sama, zaku iya rasa wuta na kwana goma. Zaka samu akwai kasashen Afrika (African Countries) da ana ruwa da iska amma baa dauke musu wuta (NEPA) wanda Najeriya ita uwa bada mama a Afrika, munfi kowace kasa karfin tattalin arziki a Afrika, amma baa amfani da kudaden ta yadda ya kamata.

Bayan dinbin kudaden da aka kashe a baya domin inganta wutan lantarkin (NEPA) amma ba biyan bukata. Yanzun wata sanarwa da kungiyar masu raba wutan lantarki a Najeriya (Association Of Nigeria Electricity Distributors – ANED) suka fitar, sunce kafin wutan lantarki (NEPA) ya inganta a Najeriya sai an kashe dalan Amerika biliyon dari daya ($100b) wanda daidai yake da kudin Najeriya Naira tiriliyon talatin da shida (N36 trillion) kafin zaa dinga samun wutan lantarki na awa ashirin da hudu (24hrs) a Najeriya. Bani da shakka wannan kudin zaiyi wuyan samu saboda ya kai kasafin kasa (Budget) Najeriya na shekara hudu zuwa biyar (4-5yrs Nigeria Budget).

Bana shakka ko akwai kudin, kuma a ware sama da wannan kudin da suka fada, idan aka basu ba za’a samu wuta na awa hudu (24hrs) a Najeriya ba. Domin kawai wawure kudin za’ayi. Domin daga gwamnatin Olusegun Obasanjo zuwa gwamnatin Goodluck Jonathan ance naira tiriliyon goma sha daya (N11 trillion) aka kashe a maganan inganta wutan lantarki (NEPA) wanda idan akayi lissafi darajan Naira a wannan lokacin ya kai kusan tiriliyon talatin da shidan (N36 trillion) da ake magana yanzun. Amma har yanzun wutan lantarkin (NEPA) bai inganta ba.

Bayan sace kudaden inganta wutan lantarkin da masu mulkin suka yi, ana kuma zargin akan wadanda suke da ikon gyara wutan da cewa akwai abin da suke amfana dashi na rashin ingantar wutan koma bayan sace kudaden da suke yi. A wata majiya ance suna da hannayen jari a masana’antun da suke samar da injin din samar da wutan Lantarki wato (Generators), akwai kuma wadanda da su suke shigo da Injinan Najeriya saboda haka a duk lokacin da aka ce wutar lantarki ya inganta a Najeriya to dole harkokin nasu zasu tsaya. Saboda da haka duk yadda zasu yi suga matsalar wutan lantarki bai kare a Najeriya ba zasu yi saboda biyan bukatunsu.

2 – Illan Matsalar Watan Lantarki A Najeriya

Matsalar wutan lantarki a Najeriya na daya daga cikin abinda ya taimaka gurin talauci da rashin aikin yi a Najeriya.

Matsalar wutan lantarki ya taimaka gurin rufe wadansu masana’antun (Companies) wanda sanadiyan rufe su mutane da dama sun rasa ayyukansu. Bayan haka da masana’antun suna aiki, koma bayan wandanda suke aiki a gurin wadansu zasu sake samun aiki a gurin, ga kuma wadanda suke kasuwanci sayarda abubuwa a wannan masana’antun duk suma hanyan su ya toshe.

Haka idan muka koma farnin masu sana’ar hanu kamar tailoli, masu walda, masu aski, da duk wani aikin da ya shafi na’ura mai kwakwalwa (Cafe) da sauransu, duk sana’une wanda suke fuskantar matsaloli sakamakon matsalan wutan lantarki (NEPA). Masu sana’ar sukan kashe mafi yawan abinda suke samu a gurin sayan man fetur da bakin mai da Gas da kuma gurin kyaran (Generator).

Idan muka duba wadannan abubuwan zamu fahimci cewa matsalar wutan lantarki ya taimaka gurin talauci da rashin aikin yi a Najeriya. Yana da kyau ace gwamnati susa maganan inganta wutan lantarki (NEPA) da gaske ta yadda zasu yi maganin duk masu kawo tseko a gurin gyara wutan.

Inganta wutan lantarkin (NEPA) shine zai ba masu niyar gina masana’antun (Companies) karfin jikin ginawa, domin duk ba masana’antar da zata so ace tana amfani da (Generator) sai ya zama dole, saboda amfani da Injinan (Generator) yafi tsada kuma bazai biya bukata kaman wutan NEPA ba.

Idan har gwamnati da inganta wutan lantarki, yan kasuwa suka gina masana’antun (Companies) zai taimaka gurin rage rashin aikin yi da talauci a cikin al’umma.

3 – Shin Ya Dace Gwamnati Ta Karbe Harkan Wutan Lantarki (NEPA) daga Hanun ‘Yan Kasuwa?

Ba shakka akasarin kasashen da suka ci gaba harkan wutan lantarkinsu (NEPA) a hanun yan kasuwa ya ke, amma abin dubawa a lamarin yan kasuwan dake gudanar da harkan wutan lantarkin Najeriya shine;

4 – Shin hanyar da aka bi na sayar da wutan (NEPA) yana kan tsari, an cika ka’idodin da ya kamata?

5 – Shin mutanen da aka sayar musu dashi su cancanci a sayar musu dashi, kuma suna yin abinda ya dace domin inganta wutan (NEPA)?

6 – Shin tun daga lokacin da aka sayar musu da shi kwalliya ta biya kudin sabulu, an samu canji akan baya?

Wadannan abubuwa guda uku ya kamata a duba su kafin ayi maganan karbe wutan (NEPA) kokuma a gyale su dashi.

Maganan ka’idodin da aka bi na sayar da wutan (NEPA) ni bani da masaniya ko an cika ka’idodin da ya dace.

Amma idan muka duba suwa aka sayarwa da harkan wutan, shin sun shiryawa harkan wutan, zamu iya cewa wadanda aka sayar musu basu dace da harkan ba domin ba harkan bane a gaban su, kawai sunyi amfani da daman da suke da shi ne suka saye harkan wutan. Saboda duk wani abinda ya shafi maganan gyara wutan a lokacin da ya lalace su basu san shi ba, kawai a basu kudi suka sani. Saide kawai kullum su dinga karawa mutane kudin wuta (NEPA) kuma ba wutan. Idan baka biya ba ace ana binka bashi kuma kai baka maga wutan ba balle ka amfana dashi.

Saboda haka mika harkan wutan lantarkin da gwamnati ta yi ma ‘yan kasuwa kwalliya bata biya kudin sabulu ba. Kawai zaluntar al’umma suke yi.

Saboda haka muna goyan baya da bawa gwamnati shawara da ta karbe wutan daga hanun ‘yan kasuwan domin cutar da ‘yan kasa kawai suke yi. Kullum a kara kudin wuta suke ba kuma wutan. Yau ko wuta zaa kai yankinku duk wani abinda za’ayi amfani dasu kama daga waya, transformer, folwaya ku zaku saya. Su basu san sayan komai ba, idan kuma kunce zaku jira su saya, wallahi sai kufi shekara baku da wuta ko a jikinsu. Domin su basu son su kashe kudi amma suna son kudi ya shigo. Shi kuma kasuwanci dole sai ka kashe kudi kafin kudi ya shigo.

Saboda haka dan Allah gwamnati tayi kokari ta karbe wutan nan daga hanun ‘yan kasuwa ta kuma inganta wutan, sai a samu saukin rayuwa.

Share.

game da Author