Kotun dake Mapo a Ibadan jihar Oyo ta warware auren shekara 11 dake tsakanin Barakat Ibrahim da Jimoh Ibrahim saboda rashin da’a da kazantar tsiya.
Babban dalilin raba wannan aure da kotun ta yi shine gano cewa duk su biyun basu kaunar juna kuma.
Alkalin kotun Ademola Odunade ya umurci Barakat da ta ci gaba da kula da dan da suka haifa mai shekaru takwas sannan shi kuma Jimoh zai biya kudin makaranta da Naira 5,000 duk wata domin ciyar da yaron.
Jimoh Ibrahim dake zama a Oja-Oba a Ibadan ya shigar da kara a kotun ne saboda rashin da’a da kazantar matarsa Barakat.
Ya ce har karuwanci Barakat tana yi sannan ta kan bi masoyan ta wurare masu nisa har zuwa kasar Ghana su hole abinsu.
“ A shekaru 11 da na yi tare da Barakat na yi ta hakuri da ita ne ko Allah ya sa ta canja amma ina. Nike wanke-Wanke da sharan gida, sannan idan ta dawo daga yawonta sai ta rika guma mini rashin mutunci ba bu abin da ya dameta.
Barakat bata musanta duk korafin da Jimoh ya fada a kanta ba sannan ita ta yarda kotu ta warware auren su.
Ta ce wannan ba shine karon farko ba da Jimoh ke neman dalilin sakinta. Ko a baya idan muka samu sabani, nine nake bin Jimoh har gida in yio ta rokon sa.