Almajirci a Arewacin Najeriya, Daga Al Mansour Hussein

0

Ga dukkan alamu kaso mafi yawa na al’ummar mu, basa banbance kalmar almajiri da kuma mabarata, wadannan kalmomi guda biyu kalmomi ne mabanbanta da juna, sai dai sukan hadu a wasu bangarori duba da yadda muke kallon su a zamanin mu.

Kalmar almajiri asalinta daga kalmar larabci ce ma’ana Almuhajirالمهاجر (The immigrant), sahihiyar ma’anarta mu a wajan mu shine wanda ya bar gida zuwa wani gari ko tsangaya neman karatun Alqur’ani, sannan kuma daga cikin bukatun wanda ya je neman karatun alqur’ani ba wai ya haddace ne kadai ba, yana san ya rubuta da hannun sa, a dunkule wannan shine almajiri ta fuskar ma’anarsa.

Kalmar mabarata kuma kalmar hausa ce, kuma tana hawa kan abubuwa da dama, daga ciki akwai su wadanda suke zuwa gidajen mutane neman abincin da ya ragu, akwai masu zama a gefen hanya suna adawo lafiya, akwai na kan titinan mu, akwai masu bin maikatun gwamnati, akwai wanda ma kawai in ya ga baka neman taimako to kai zaizo wajanka nema zatan sa kana da shi da dai sauransu.

Inda wadannan kalmomi suka hadu kuwa a bayyane yake, a wancan lokaci duk wanda aka kaishi almajirci to kowanne lokacin gama abincin rana da na dare zasu fita neman abinci, kasantuwar da wuya ka samu cikakken gida suna yin abinci daidai iya bukatar su, ana girka abinci da tinanin bako zai iya zuwa, hakan ka iya sawa almajiri ya samu rabonsa matukar yaje bayan kammala abincin.

Kuma Malaman makarantun Allo da dama suna da sana’o’in su musamman kasuwanci da noma, wanda da su suke rufawa kan su asiri ta fannin bukatu na rayuwa. Haka kuma da dama suma almajiran nasu indai sun mallaki hankalin kansu, basa zaman banza, zaka same su suna kananan sana’o’i kamar su dinki hula saye da sayarwa a ranaikun da kasuwanni mafiya kusa da su suke ci.

Wadanda kuma suke barin kauyuka zuwa birane, zaka same su suna kokarin kiyaye kima da mutuncin karatun na Alqur’ani wanda sanadin sa suka bar garuruwan su da gidajen su, wanda a karshe zaka same su sun zama malamai na alqur’ani mahaddata kuma suna iya rubuta shi da hannun su, abin lura anan shine baza ka iya tantance wanda yazo almajirci da mazaunin gari ba saboda tsafta da ake da ita a wancan lokacin.

Halin da muke ciki yanzu kuwa duk ya sha banban da wannan tsari da muka riska ana yi a lokutan na baya. Ba duka aka taru aka zama daya ba, har yanzu akwai masu tsari a Malaman mu na allo sai dai akwai kuma gurbatattu, kamar yadda kowa ya sani baka iya tsaftace komai dari bisa dari dole a samu wanda bazai tsaftatu ba.

Da yawan iyaye a yanzu ba suna kai yara karatu bane dan samun karatun Alqur’ani mai tsarki sai dan rage nauyin yaran da suka haifa da kuma dorawa wadanda basu suka haife su ba, yana cikin dalilin kai yara kanana bara almajirci birane wadanda basu kai ko da shekara biyar da haihuwa ba, wanda zaka samu yaro baya iya samun abincin da zai ci ballantana kayan da zai sa ingantacce kuma tsaftatacce, to a irin wannan yanayi yaro bazai samu karatun ba, idan kuma akayi rashin sa’a ya hadu da bata gari sai tarbiyar sa ta lalace ya zamarwa al’umma annoba.

Karatun Allo

Karatun allo yana da muhimmanci da idan akace babu shi a yanzu, to zamu wayi gari babu wanda zai iya haddace shi da kuma ya rubuta shi ba tare da kuskuren ko da wasali ba, hakan ya samo asali daga farkon koyansa, misali farawa da babbaku sannan farfaru, daga bisani ya kasance zaka iya hada baki ka karanta da kanka, haddar allo tana da banbanci da haddar karatun islamiyya.

Duk lokacin da ake magana akan barace barace tinani ya daina takaituwa akan almajiran makarantun allo, sai dai lallai suna daukan kaso mafi tsoka acikin al’amarin.

Za’a iya hana barace barace da kuma tsaftace makarantun allo ta hanyoyi da dama, daga ciki akwai ta hanyar Hakimai, Dagatai da kuma masu unguwanni, ayi dokoki akan iyayen da ke kai yaransu makarantun allo ba tare da tallafawa malaman ba, da kuma daukar nauyin wahalhalun yaron, ta fuskar abinda zai ci, sabulun wanka suturar da zai sa da sauransu. Abu na gaba dole ne ya zama da hadin gwuiwar gwamnatocin arewa, domin bazakayi a wata jiha ba wata kuma batayi ba a samu abinda ake nema.

Dukkanin wannan ra’ayoyi na ne na kashin kaina a matsayina na wanda ya fito daga gidajen Karatun Al’qur’ani, ta bangaren Iyaye na da Kakanni na. Allah muna rokon ka, ka taimaki duk mai san kawo gyara a wannan al’amari da kyakkyawar manufa, Allah ka karfafi gwuiwar duk Gwamnati me kyakkyawan kuduri akan addininmu na musulunci. Amin.

Mansur Hassan Hussaini (mansurkust@gmail.com)

Share.

game da Author