KATSINA: An damke DPO da budurwar sa bayan mutuwar ’yar aikin gidan sa

0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta bada sanarwar damke DPO na Karamar Hukumar Mashi da ke cikin Jihar dangane da mutuwar mai aikin gidan sa.

An damke DPO Garba Talawai tare da wata budurwar sa mai suna Sadiyya Danyaya, bisa rasuwar mai aikin ta sa ’yar shekaru 16 kacal da haihuwa.

Kakakin Yada Labarai Gambo Isa ne ya sanar da haka a cikin wata takardar da ya sanar wa manema labarai yau Asabar a Katisna.

“Kansilan Karamar Hukumar Mashi ne mai suna Abubakar Haruna, ya sanar wa DOP din cewa an ga wata gawar yarinya a cikin daji a Mashi.

“DOP da sauran tawagar jami’an tsaro sun je wurin inda suka dauki gawar suka kai ta wani karamin asibitin duba marasa lafiya, wand aba na kwantarwa ba ne.

“Daga baya sai aka gano cewa gawar wata yarinya ce mai suna Rabi Abdullahi, wadda ’yar aikin Sadiyya Danyaya ce. Sadiya kuma budurwar DOP din ce.

“Wasu jami’an kula da lafiya a karamin asibitin sai suka shaida gawar cewa, ai kuwa it ace gawar da DOP din da wani dan sanda suka kai kwana daya da wuce, amma jami’an asibitin suka tabbatar musu da cewa ai matacciya ce.

“Sun ce an kai yarinyar a jiya Juma’a ne a cikin wata mota kirar Toyota Carina II, mai launin ja, wdda aka tabbatar cewa ta DPO din ce.”

Haka Kakakin Yada Labarai na ’Yan Sandan Katsina, Gambo ya shaida wa ‘yan jarida.

Ya kara yin bayanin cewa bincike ya nuna cewa Sadiyya budurwar DPO din ta kai masa rahoton cewa ba ta ga yarinyar ba kwanaki biyu, tun bayan fadan da ta yi mata saboda an dirka mata cikin-shege.

“Binciken farko-farko ya nuna cewa an samu DOP da laifin boye wani abu dangane da dalilin mutuwar yarinyar.”

Tuni dai Kwamishinan ’Yan Sanda ya umarci da a gudanar da kwakkwaran bincike.

Kwamishinan ‘Yan Sanda Buba ya shaida cewa DPO din da budurwar ta sa sa duk su na bada hadin kai ga masu binciken gano gaskiyar lamarin.

Ya kuma tabbatar wa jama’a da iyayen yarinyar da ta mutu din cewa za su tabbatar da mai laifi, kuma za a hukunta duk mai hannuna cikin dalilin mutuwar yarinyar.

Tuni dai har an tura wani babban jami’in dan sanda a Mashi, a matsayin sabon DOP na Karamar Hukumar ta Mashi.

Share.

game da Author