Jirgin Air Peace ya rufta cikin jeji cike da fasinjoji a Fatakwal

0

Jirgin kamfanin Air Peace mai lambar tashi P47291, ya samu tangardar kasa sauka filin saukar jirage na Fatakwal lami lafiya.

Air Peace, wanda ya tashi yau Asabar daga Abuja zuwa Fatakwal, ya isa birnin yayin da ake tsuga ruwan sama kamar da bakin-kwarya.

Duk da kokarin cin burki da matukin jirgin ya yi, sai da ya zarce ya shiga jeji tare da fasinjojin ciki.

Sai dai kuma rahotanni daga hukumomi daban-daban sun tabbatar da cewa babu asarar rayuka, kuma babu cin raunuka.

Hadarin ya faru wajen karfe 3:42 na yammacin yau Asabar.

Henrietta Yakubu, wadda ita ce Babbar Manajan Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Kasa, ta bayyana cewa hadarin ya faru, amma babu wanda ya rasa ran sa.

Ta ce duk da jirgin ya kauce hanya ya afka cikin jeji, direban ya yi kokari kwarai wajen mazgayawar da ya yi wa jirgin ya tsaida shi.

A cewar Yakubu, duk da ruwan da ake tsugawa kuma ga shi kasa ta jike jagyaf, hakan bai sa karkashin jirgin ya shige cikin kasa ba.” Inji ta.

Sai dai kuma Babban Jami’ain Ayyukan Peace Air mai suna Oliwatoyin Olajide, ya danganta ruftawa cikin daji da jirgin ya yi da yanayin yadda ruwa ya yi ambaliya ya cika kan titin saukar jirgin.

Ya yaba wa kwarewar direban jirgin wanda ya ce cikin ‘yan dakikoki kadan ya yi sauri ya tsaida jirgin kuma kowa ya fita lafiya.

Tuni dai an damka jirgin a hannun hukumar kula da lafiyar jirage ta kasa domin ta caje shi ta ga yanayin lafiyar sa.

Share.

game da Author