Malaman zabe da dama sun bayyana cewa lallai sun aika da sakamakon zabe da yawan mutanen da aka tantance da wadanda suka kada kuri’a rumbun tattara ajiya na hukumar zabe dake Abuja.
Da yawa daga cikin su da suka tattauna da PREMIUM TIMES sun bayyana cewa tun daga tantance masu zabe zuwa wadanda, jefa kuri’a da sakamakon duk sai da muka suka aika rumbun.
” Mun rika aikawa da sakamakon zabe zuwa rumbum ajiya dake Abuja. Wannan shine horon da aka yi mana kafin zabe. An gaya mana mu tabbata mun aika da sakamakon zabe da duk wani abu da muka yi da na’urar tantance masu zabe zuwa Abuja.
” Sai dai mun rika samun matsala a dalilin netwok na yanar gizo. A wasu lokuttan ba mu iya turawa saboda babu sabis.
Wasu kuma da dama sun su sun rika ba wadanda suka mika wa wannan na’ura kudi ne domin su taya su tura sakon zuwa rumbun.
” Duk da an babu takardun da zamu rubuta sakamakon zabe a ciki, an umarcemu da mu mu tura zaben zuwa wannan rumbu.
Malaman zabe a jihohin Osun, OYo Sokoto duk sun bayyana cewa sun bi umar nin hukumar wajen aikawa da sakamakon zabe rumbun ajiya dake Abuja.
Amma kuma i da aka rika samun matsala baya ga aikawar mun gano da dama bau iya aika wa da sakamakon ba. Abaya munce an samu matsalar sabis na Intanet, hakan ya sa wasu da dama mika na’ urar suka yi ba tare da sun auka da komai ba.
Ban yi amfani da Rumbu ba
Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya musanta kalaman da aka rika dangantawa da shi cewa akwai rumbun ajiyar alkaluman zabe ko a lokacin da ya yi shugabancin hukumar a lokacin zaben 2015.
A cikin wani sakon tes da wani hadimin Jega ya turo wa PREMIUM TIMES a madadin sa, Farfesa Jega ya jaddada cewa tun daga lokacin da ya yi shugabancin INEC har ya sauka, babu lokacin da suka taba tattara sakamakon zabe a rumbun ajiyar sakamakon zabe na intanet, wato ‘server’.
“Wannan wata karya ce ake kantara mini ko aka kitsa mini. Ban taba cewa INEC a lokaci na mun tattara bayanan sakamakon zaben ta intanet, wato rumbun ajiya na ‘server’ ba. Domin a tsarin Dokar Zabe, laifi ne a tattara sakamakon zabe ta kafar sadarwar zamani, wato ‘server.’
“Na kasa gane dalilin da zai sa wasu gafalallun mutane za su zauna su kirkiri karya a danganta ta da ni. Su ce na ce abin da ban ce ba. Saboda ban taba fadin haka ba. Karya ce kawai su ke yi.”
Haka raddin da Jega ya aiko ga PREMIUM TIMES ga wadanda ke cewa ya ce sun yi amfani da ‘server’ a lokacin da ya ke shugabancin INEC.
Sai dai kuma duk da wannan karyatawa da Jega ya yi, wannan rikita-rikita za ta dade ana tattaunawa kan ta.
Mun yi gwajin ‘Server’ a 2018
Kwamishinan Zabe na Kasa, Solomon Soyebi yace INEC ta yi amfani da ‘server’, amma a matsayin gwaji ba wai tattara sakamakon zabukan 2018 da aka maimaita. Amma ba tattara zabe 2019 aka yi a cikin ta ba.
Abinda Hukumar zabe ta ce game da rumbun tattara sakamakon zabe
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana wa Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa cewa ba ta mallaki wani runbun tattara bayanan sakamakon zabe da a Turance ake kira ‘server’ ba.
Wannan bayani ya biyo bayan karar kalubalantar zaben shugaban kasa da PDP tare a dan takarar ta Atiku Abubakar suka shigar da APC, Shugaba Muhammadu Buhari da kuma INEC kan ta.
A cikin karar da Atiku ya shigar, ya yi ikirarin cewa sakamakon da INEC ta bayyana daban, wanda ke cikin rumbun tattara sakamakon zaben ta kuma, wato ‘server’ daban.
Atiku ya yi ikirarin cewa shi ne ya yi nasara a kan Buhari da ratar kuri’u masu yawa, kamar yadda ya ce ita ‘server’ din ta nuna.
Daga nan PDP da Atiku sun nemi kotu ta ba su damar duba wannan rumbun ajiyar kididdigar alkaluman zabe, wato ‘server’ da suka yi ikirarin INEC ta mallaka.
Sai dai kuma lauyan INEC mai suna Yunus Usman, ya roki kotu ta yi watsi da wannan zargi, domin har ma gara tatsuniya da shi. Ya ce INEC ba ta da wata ‘server’ da ta tattara sakamakon zabe, kamar yadda PDP da Atiku suka yi zargi.
Ba za mu bada abinda bamu da shi ba
Lauyan INEC Usman ya ci gaba da cewa abin akwai daure kai, domin Atiku da PDP na son INEC ta ba su abin da ba ta da shi, kuma abin da ba ta taba yi ba, ballantana har a ce INEC ta mallake shi.
“Su fa so suke yi mu ba su abin da mu kuma ba mu da shi.” Inji Usman.
Daga nan kuma ya jawo hankalin kotu a kan hukuncin da ta yanke ranar 6 Ga Maris, inda ta bai wa PDP damar duba kayan da aka gudanar da zaben 2019, wanda babu maganar rumbun tattara sakamako, wato ‘server’ a ciki a lokacin.
Dukkan lauyoyin Shugaba Buhari, wato Wole Olanipekun da kuma na APC, wato Lateef Fagnemi sun nemi a kori rokon da PDP da Atiku suka yi.
Zargin da PDP da Atiku suka yi ya nuna a cewar su sun samu bayanan sakamakon zaben da suke ikirari ne a cikin wannan rumbun ajiya mai lamba: “INEC_PRES_RSLT_SRV2019, kuma mai adireshin Mac 94-57-A5-DC-64-B9 wanda ke da lambar Microsoft ID 00252-7000000000-AA535.” Inji su Atiku.