Duk da kin zabe na da mutanen Abuja suka yi, zamu tabbata sun samu aminci – Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa tawagar da suka ziyarce shi gaisuwar Sallah a fadar shugaban Kasa cewa duk da mutanen babban birnin tarayya basu zabe shi ba a 2019, zai maida hankali wajen inganta garin.

Tawagar wanda mataimakin shugaban kasa ya jagoranta sun kai ziyara ne domin taya shugaba Buhari murnar sallah karama.

A jawabin sa Buhari ya yabawa mataimakin sa Yemi Osinbajo bisa kwazo da maida hankali da yayi wajen tallata manufofin gwamnati mai ci yana mai cewa ” Idan ba haka kayi ba to za a iya samun matsala matuka domin kuwa zai zamo kamar gwamnati bata komai kenan.

Bayan haka kuma sai a cikin barkwanci ya ce wa sanata Philip Aduda dake wakiltar Abuja a majalisar dattawa cewa ya hango shi amma fa bai manta yadda suka tabbata ya fadi zabe a Abuja ba.

A Cikin raha sai Buhari yace duk da kin zaben sa da mutanen Abuja suka yi, ba zai sa aki maida hankali wajen tabbatar da ganin garin ya inganta ko kuma ya shaharaba domin mutanen da ke cikinta su wataya da kuma kasa baki daya.

Ana shi jawabin, mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya yi kira ga shugabannin addinai da su tabbata sun maida hankali wajen kira ga mabiyansu da a rungumi juna duk da banbancin addini da kabila da ya raba mu.

Ya ce dole a hada kai don ganin an kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan.

Wadanda suka biyo wannan tawaga sun hada da Shehu Umar Galadanci, na babban masallacin Abuja, tsohon gwamnan jihar Ribas Rochas Okorocha, Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, Janar Abayomi Olonisakin da Janar Tukur Buratai.

Sauran sun hada da Babban hafasan sojojin ruwa da na sama Ibok-Ete Ibas, Sadique Abubakar, Sufeto janar din yan sanda Mohammed Adamu, Babagana Monguno, Yusuf Magaji Bichi, da gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emiefiele da dai sauran su.

Kafin nan shima maitaimakawa shugaba Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmed ya yi wa shugaba Buhari tattaki ta musamman domin yi masa gaisuwar Sallah.

Share.

game da Author