A ci gaba da buga wasan kwallon kafa na cin kofin nahiyar Afrika da ake yi a kasar Masar, kasar Tunisia ta buga kunnen doki da kasar Angola a wasan ranar Litini.
An tashi wasa 1-1.
Itako kasar Afrika ta Kudu ba ta yi sa’a bane inda ta sha kayi a hannun kasar Ivory Coast da ci daya mai ban haushi.
A ranar Lahadi kuwa, kasar Senegal ta doke Tanzania da ci 2 babu ko daya.
Algeria 2, Kenya 0, Morocco 1, Namibia 0.
A gobe Talata kuma za a kara ne tsakanin kasar Kamaru da Guinea-Bissau, da kuma Kasar Ghana da Benin.
Discussion about this post