Wasu likitoci da suka kware a sa ido a halayen mutum daga jami’o’in Azusa Pacifi da UC Merced dake kasar Amurka sun gano cewa mace daya daga cikin mata uku na yin soyayya ne da maza ko mace saboda dan abinda za su samu na abinci da kudin kashewa.
Sakamakon binciken ya kuma nuna cewa kashi 23 zuwa 33 bisa 100 daga cikin matan da zama kullum a yanar gizo suna haka nek o kila wani ya taya, yace yana so.
Sannan kuma bisa ga wannan bincike, kusan duka ire-iren wadannan mata kan fada soyayya da wani namiji ne idan suka tabbatar yana da dan abin hannu, wato kudi.
SAKAMAKON BINCIKEN
Brian Collisson,Jennifer Howell da Trista Harig ne suka gudanar da wannan bincike.
Adadin yawan matan da suke soyayya da jinsin mata irin su sun kai 820, sannan da dama kuma galantoyi suke kawai a yanar gizo basu da wani wanda ya nuna yana so ko kuma yayi tayi, sannan wasu kuma suna da masoya mace ko namiji.
A wani kashin kuma an samu matan dake soyayya da maza zalla da suka kai 357.
A takaice dai sakamakon binciken ya nuna cewa mata da maza da yawa sun ce ba suga laifin mutum ya fada tsundum cikin soyayya ba don abinda zai samu a wajen abokin soyayyar sa wato wanda ya ke so.
Irin wadannan masoya idan fa babu wani abu da za su samu a wurinka to fa fatali da kai zasu yi su kara gaba domin bashi bane a gaban su, sun fito neman farantin shikafa ne da tsoka da dan kudin kashewa ba soyayyar dali-dalin ba.
A wajen irin wadannan mutane duk soyayyar da ba zai haifar musu da kudi ko wani abin more rayuwa ba basu yin shi.