Kotun dake jihar Ekiti ta daure wani faston darikan cocin ‘Methodist’ Peter Adewuyi mai shekaru 30 a kurkuku bisa laifin shirya a yi garkuwa da shi na karya.
Alkalin kotun Omolola Akosile ya kuma daure abokin Peter mai suna Oluwadare Ajewole mai shekaru 25 a kurkukun har sai kotu ta kammala sauraren karan a bisa laifin taya Peter shirya yin garkuwa dashi na karya.
Ya kuma daga shari’ar zuwa ranan 24 ga watan Yuli.
Lauyar da ta shigar da karar Monica Ikebuilo ta bayyana cewa Peter ya shirya da abokinsa Ajewole yaje ya boye cewa anyi garkuwa da shi ranan 11 ga watan Yuni.
Bayan shirya wannan karya sai Ajewole ya fada wa cocin cewa wai an yi garkuwa da Peter a hanyar Ijebu Jesa da Aramoko sannan har ana bukatan Naira miliyan uku kudin fansa.
Ajewole ya bayyana wa mambobin cocin da su taimaka asamu a hada wannan kudin fansa da masu garkuwan ke bukata kafin su kashe shi.
Monica ta ce asirin Peter da Ajewole ya tonu ne a lokacin da ‘yan sanda suka kama Peter a wani Otel dake Ado Ekiti yana sheke ayarsa kawai babu ruwan sa.